fbpx
Friday, January 21
Shadow

Burin Tinubu Na Zama Shugaban Kasa Babban Abin Dariya Ne, Bode George

Daga Ibrahim Da’u Mutuwa Dole

Jigon jam’iyyar PDP, Cif Bode George, ya bayyana burin shugaban jam’iyyar APC Asiwaju Bola Tinubu, a matsayin babban abin dariya.

George ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da ya yi da jaridar The PUNCH a ranar Litinin yayin da yake mayar da martani kan matakin da Tinubu ya dauka na sanar da shugaban kasa, Muhammadu Buhari aniyarsa ta tsayawa takara.

A bayanin George yace; “Wannan abin da ake kira buri dole ne ya zama babban abin dariya, Shugabancin Najeriya ba na masu hali irin su Bola Tinubu bane, Kalli yadda ya karkatar da dukiyar jihar Legas.

Abin mamaki shi ma yana iya mafarkin zama shugaban Najeriya,” in ji George.

George ya ce yankin Kudu maso Yamma na da ingantattun shugabanni da za su iya samar da shugaban Najeriya na gaba, Sai dai ya ce Tinubu ba ya cikin su.

Ya ce zai zama cin fuska ga yankin kudu maso Yamma, wanda shi ne yankin da ya fi kowa zamani a kasar nan, idan aka yi wa Tinubu sulhu.

George ya kuma ce abin takaici ne a ce wuri mai tsarki kamar fadar shugaban kasa ta zama wurin da Tinubu zai bayyana burinsa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *