fbpx
Wednesday, October 20
Shadow

CAN: ‘Gwamnati ta sake nazari kan janye sojoji’

Kungiyar kiristocin Najeriya CAN, ta bukaci gwamnatin kasar ta nazari kan shirin ta na fara janye sojoji daga wasu yankuna da tace an samu saukin matsalar tsaro a cikin su.

Mataimakin shugaban kungiyar na arewacin Najeriya Rabaran Joseph John Hayepp, ya shaidawa BBC ce wa har yanzu akwai matsalar tsaro a yawancin yankunan kasar, don haka janye dakarun soji don maye gurbin su da ‘yan sanda ba karamar kasassaba bace.
Rabaran Joseph ya ce jihohi kamar Kaduna da Filato da Benue da Taraba har da Abuja babban birnin Najeriya har yanzu akwai kalubalen tsaro a cikin su.
”Idan har hakan ta faru, muna zaune muma wataran bara garin zasu so su sace mu,” inji shi.
Gwamnatin Najeriya dai tace zata janye sojojin ne don maye gurbin su da yan sandan, sai dai wai ‘yan kasar na ganin a sake nazari kafin janye su baki daya.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Rabaran Joseph ya kara da cewa; ”wasu jami’an ‘yan sandan basu da isassun kayan aikin da zasuyi amfani dashi don tsare rayuka da dukiyoyin jama’ar jihohi idan bukatar hakan ta taso.”

A karshe CAN ta bukaci gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, ta dakatar da shirinta kamar yadda ta tsara yi a farkon shekarar 2020.

A karshen watan jiya ne, gwamnatin Nijeriya ta yi wannan sanarwa, tare da kafa hujjar harkokin tsaro sun inganta yankunan da a baya su ke cikin matsanancin rashin zaman lafiya.

Ko da yake, hukumomi ba su fito kai tsaye sun bayyana yankunan da za su janye sojojin daga cikinsu ba, amma CAN ta nemi su sake nazari.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *