fbpx
Thursday, May 6
Shadow

Gist/Social Media

Bidiyo:Kalli yanda Matasa suka daure wani a jikin Itaciya suka zaneshi sosai bayan dukan rashin Mutunci da yawa wata Tsohuwa

Bidiyo:Kalli yanda Matasa suka daure wani a jikin Itaciya suka zaneshi sosai bayan dukan rashin Mutunci da yawa wata Tsohuwa

Gist/Social Media
A bidiyon, an ga mutumin yana amfani da doguwar sanda yana yi wa tsohuwar bulala, ya kada ita ƙasa, ya cigaba da dukanta. An bayyana mutumin a matsayin Sunday Maduegbunam Kosisochukwu daga Ogidi a jihar Anambra. An ga makwabta suna rokonsa amma sam yayi burus da maganarsu ya cigaba da dukanta. Saidai matashi ya gamu da fushin matasan garin bayan da suka ga bidiyon, suka kuma tambaye ko da gaske shine a bidiyon? Ya amsa cewa shi ne tare da neman gafararta. Duk da hakan matasan sun hukunta shi ta hanyar taure hannayensa da kafafunsa kan icce, kuma sukai ta zabga masa bulala. Kalli bidiyon a kasa;
Wata yarinya ‘yar shekaru 13 da haihuwa ta kashe kanta a Calabar

Wata yarinya ‘yar shekaru 13 da haihuwa ta kashe kanta a Calabar

Gist/Social Media
Wata yarinya ‘yar shekaru 13 da aka bayyana da suna Nsebong ta kashe kanta a Calabar, babban birnin jihar Kuros Riba. A cewar mai yada labaran FadFM Calabar, Archibong Efefiom, lamarin ya faru ne a yankin Diamond Hill na Calabar da yammacin Lahadi, 2 ga Mayu. An bayyana cewa, bayn iyayen yarinyar sub tayar jijiyoyin wuya game da batan ta, sai Maƙwabta suka taru suka shiga bincike sai kawai suka gano gawarta rataye a gini A halin yanzu an gayyaci jami'an yan sanda domin gudunar da bincike akan lamarin.
Ban ga alamun cikar imani a wajen Malaman Musulunci na Nijeriya ba – Ummi Zee-Zee

Ban ga alamun cikar imani a wajen Malaman Musulunci na Nijeriya ba – Ummi Zee-Zee

Gist/Social Media
Fitacciya kuma tsohuwar jarumar masana'antar Kannywood, Ummi Ibrahim wacce aka fi sani da Ummi Zee-Zee tace ba ta ga alamun cikar imani a wajen Malumman Musulunci na Nijeriya domin kuwa a lokacin da tayi ikirarin cewa zata kashe kanta babu wani daga cikin su da yayi mata nasiha sai dai zagi tsinuwa. Ummi Zee-Zee ta bayyana haka ne a wani saƙo da ta walla shafinta na Instagram a yau bayan ziyarar da ta kai wa Kwamishinar Harkokin Mata ta Jihar Kano, Dakta Zahra’u Muhammad, bisa gayyatar ita kwamishinar. Karanta cikakken sakon a kasa;
Wani malamin Jami’ar Danfodiyo dake Sokoto, matarsa da yaransa 2 sun mutu a wani mummunan hatsari mota

Wani malamin Jami’ar Danfodiyo dake Sokoto, matarsa da yaransa 2 sun mutu a wani mummunan hatsari mota

Gist/Social Media
Wani malami a sashen Kimiyyar Jinya na Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato, Malam Tajuddeen Musawa, da matarsa ​​Zainab Abubakar da ’ya’ya biyu sun mutu a hatsarin mota. An ce dan asalin jihar Katsina tare da iyalansa suna kan hanyarsu ta zuwa garinsu daga jihar Sakkwato don halartar jana’izar kakansa lokacin da hatsarin ya faru. Wata sanarwa da shugabannin jami’ar suka bayar a ranar Lahadi, 25 ga Afrilu, ta ce hatsarin ya afku ne a karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara a ranar Asabar, 24 ga Afrilu. Yan uwa da abokan arziki sun shiga shafin sada zumunta na Facebook domin jajantawa. Duba bayanan a ƙasa:
Muna tare da Pantami>>Fadar Shugaban kasa

Muna tare da Pantami>>Fadar Shugaban kasa

Gist/Social Media, Siyasa, Uncategorized
Fadar Shugaban kasa ta bayyana cewa, tana tare da Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Sheikh Isa Ali Pantami kan kiraye-kirayen da ake na cewa a saukeshi.   Hakan ya fito ne daga bakin kakakin Shugaban kasa, Malam Garba Shehu inda yace sun amince da jawabin da Pantami yayi na cewa lokacin yana karamin yaro ne yayi waccan magana kuma tuni ya canja matsayi.   Garba Shehu yace maganar da ake ta Pantami ya sauka ba aka abinda ya fada a baya bane, game da aikinsa na yanzu da yake ne.   Yace Kuma Pantami ba zai sake maimaita waccan magana ba. “Today, there is an unfortunate fashion in public discourse that makes leaders in politics, religion, and civil society liable in the present for every statement they have ever made in the past – no matter ho...
Hukumar ‘yansanda ta haramta al’adar yin tashe a Kano

Hukumar ‘yansanda ta haramta al’adar yin tashe a Kano

Gist/Social Media, Uncategorized
Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta haramta yin tashe a daukacin jihar Kano baki daya. Mai magana da yawun rundunar yan sanda ta jihar Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana haka ga manema labarai a Kano. Dsp Abdullahi Kiyawa ya ce rundunar ta gargadi iyayen yara da ‘yan mata da samari da su guji saba dokar. Indai ba'a manta ba tashe al’adar ce da Bahaushe ke gudanarwa daga goman farko na watan azumin Ramadana. Kiyawa ya ce daukar matakin ya biyo bayan yadda bata gari ke amfani da al’adar wajen yin fadan daba da kwacen waya da ta’amali da miyagun kwayoyi. Ya kara da cewa kwamishinan ‘yan sanda Sama’ila Shu’aibu Dikko ya umarci jami’an tsaro su tabbatar jama’a sun bi dokar. Sannan ya jaddada cewa rundunar ba za ta saurarawa duk wanda ya bijirewa dokar ba....
Bidiyo: Wata mata ta lakadawa Uban gidanta duka saboda aika mata sakonnin batsa

Bidiyo: Wata mata ta lakadawa Uban gidanta duka saboda aika mata sakonnin batsa

Gist/Social Media
Matar wacce ta fito daga arewa maso gabashin China, mai suna Zhou, a cikin bidiyon ta jefa masa littattafai a fuska tare da lakada masa duka da sandar abun goge-goge yayin da yake kokarin neman gafara a wajenta. A cikin bidiyon na tsawon mintuna 14 wanda ya yadu a shafukan sada zumunta na China Weibo, an ga Zhou tana kwarara ma maigidan nata ruwa a jiki. Ta yi iƙirarin cewa an turo mata saƙonnin rubutu na batsa har sau uku, hakama abokiyar aikinta. An sallami Uban gidan nata daga aiki bayan faruwar lamarin Zhou, a cewar jarida The Independent. Zhou tayi karar Uban gidan nata ga ‘yan sanda a makon da ya gabata, kuma ana zargin hukumomi suna duba rahotonta kafin bidiyonta ya yadu. Da yawa daga cikin masu amfani da shafukan sada zumunta sun yaba mata tare da bukatar hukumom...
Hotuna: Wata mata da ba a san ko wacece ba ta mutu a cikin motar jigila a Jihar Anambra

Hotuna: Wata mata da ba a san ko wacece ba ta mutu a cikin motar jigila a Jihar Anambra

Gist/Social Media
Wata mata da ba a san ko wace ce ba ta mutu a cikin motar bas ta jigila a karamar hukumar Oyi ta jihar Anambra. Daya daga cikin fasinjojin, Gifted Joseph, wanda ya bayyana hakan a Facebook ya ce lamarin ya faru ne a ranar Alhamis, 15 ga Afrilu, a mahadar Awkuzu. A cewar Ms Joseph, lokacin da suka isa mahadar, ba zato ba tsammani matar ta fara ihu, tana cewa ba ta iya numfashi, bayan 'yan mintoci kaɗan, ta mutu. Marigayiyar ba ta da wata shaidar da za'a iya gane daga ina take amma an ce za ta je yankin Tarzan da ke Onitsha Ya kara da cewa a yanzu suna ofishin yan sanda na Ogini da ke Onitsha, za mu iya raba hotunanta, har sai mun samu wanda ya santa ko danginta. Kalli hotunan a kasa: