fbpx
Saturday, August 20
Shadow

Kasuwanci

Wahalar man jirgin sama ka iya sa mu dakatar da aiki, kamfanin jirgin sama na Ibom ya fadawa abokan fasinjojinsa

Wahalar man jirgin sama ka iya sa mu dakatar da aiki, kamfanin jirgin sama na Ibom ya fadawa abokan fasinjojinsa

Kasuwanci
Kamfanin jirgin sama na Ibom Airlines sun ayyanawa abokan fasinjojinsu cewa da yiyuwar a dakatar da wasu jiragen saboda wata 'yar matsala da kamfanin ke fuskanta. Shugaban kamfanin Aniekan Essienette ne ya bayyana hakan a yau ra ar juma'a inda yace ana samun matsalar ne saboda wahalar man jirgin sama a kasar. Amma yace zasu yi kokari su magance wannan matsalar amma fa man jirgin sama yana tsada sosai sai yanzu a Najeriya.
Yanzu Yanzu shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika ragamar kamfanin NNPC ga ‘yan kasuwa

Yanzu Yanzu shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika ragamar kamfanin NNPC ga ‘yan kasuwa

Breaking News, Kasuwanci
Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya mika ragamar kamfanin man Najeriya na NNPC ga 'yan kasuwa. Shugaban a taron da suka gudanar yau da safenan wanda aka fara da misalin karfe tara ne ya mika ragamar man fetur din ga 'yan kasuwar. Kuma yace yayi hakan ne don habaka tattalin arzikin kasa Najeriya kuma za'a ga cigaba sosai kan wannan gagarumin taron da suka gudanar. Shugaban kasar ya mika sakon gaisuwarsa ga shugaban sanatoci Ahmad Lawal da sauran ministocinsa da gwamnanoninsa da suka hallaci wannan gagarumin taron.
‘Yan kasuwar man fetur sun bijirewa gwamnatin tarayya sun kara farashin litar man fetur zuwa naira 185

‘Yan kasuwar man fetur sun bijirewa gwamnatin tarayya sun kara farashin litar man fetur zuwa naira 185

Kasuwanci
'Yan kasuwar man fetur sun bijerewa farashin da gwamnatin tarayya tace masu su riga sayar da litar mailn fetur inda suke sayar da shi akan ra'ayoyinsu. Gwamnatin tarayya ta umurci 'yan kasuwar man fetur na Najeriya cewa su riga sayar da litar man a farashin naira 165. Amma yanzu ranar alhamis kungiyar 'yan kasuwar man fetur ta MOMAN ta koka kan farashin da gwamnatin ta saka masu inda tace ba zasu fita ba idan suka sayar da shi a hakan. Kuma shima Chinedu shugaban babban kungiyar 'yan kasuwar man fetur ta IPMAN,yace farashin gwamnatin ba zai fidda 'yan kasuwa ba gaskiya, wanda hakan ne yasa yawancin 'yan kasuwar ke sayar da lita a farashin 185 har ma zuwa 195.
Twitter ta maka shahararren mai kudin duniya Elon Musk a koto saboda ya fasa sayen kafar sada zumuntar

Twitter ta maka shahararren mai kudin duniya Elon Musk a koto saboda ya fasa sayen kafar sada zumuntar

Kasuwanci
Kamfanin sada zumunta na Twitter sun maka shahararren mai kudin duniya, Elon Musk a kotun Chancery bayan yace ya fasa sayen kafar sada zumuntar. New York Daily News ne suka ruwaito wannan labarain na cewa Twitter ta maka Elon Musk a kotu saboda ya fasa sayen kafar sada zumuntar kamar yadda yayi alkawarin saya a farashin dala biliyan 44. Twitter ta maka mai kamfanin Telsa a kotu ne ranar talata amma yace yanada damar da zai iya canja ra'ayinsa na sayen kafar sada zumuntar.
Shugaba Buhari ya jinjinawa shugaban BUA bayan Kasar Faransa ta sake zabe shi a matsayin shugaban kasuwancinta da Najeriya

Shugaba Buhari ya jinjinawa shugaban BUA bayan Kasar Faransa ta sake zabe shi a matsayin shugaban kasuwancinta da Najeriya

Kasuwanci
Shugaban kasar Najeriya, Mejo janar Muhammadu Buhari ya jinjinawa shugaban kungiyar BUA, Abdul Samad Rabi'u bayan shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron ya sake zabar shi a matsayin shugaban kungiyar kasuwanci tsakanin Najeriya da Faranansa. Shugaba Buhari jinjina masa ne a sakon daya fito daga hannun hadiminsa Garba Shehu wanda yayiwa taken, 'Buhari na taya shugaban kungiyar BUA murna a sake zabar shi da Faransa tayi na shugaban kasuwancinta da Najeriya. Inda yace shugaba Buhari ya jinjina masa saboda hazakarsa da kuma aiki tukuru yasa aka zabar shi a matsayin shugabar kungiyar wadda aka kaddama shekara guda data gabata.
Hankalin Gwamnati ya tashi saboda ‘yan Najariya miliyan 33 sun shiga harkar Cryptocurrency

Hankalin Gwamnati ya tashi saboda ‘yan Najariya miliyan 33 sun shiga harkar Cryptocurrency

Kasuwanci
Rahoto ya nuna cewa, 'yan Najariya miliyan 33 ne ke harkar kasuwancin Cryptocurrency wanda hakan ya tayar da hankalin hukumomin Najariya.   Babban bankin Najariya, CBN ya saka dokar hana kasuwancin amma saidai wannan doka bata yi tasiri ba.   Maimakon ma ta hana Cryptocurrency, saima karuwa masu wannan harka suka yi, mafi yawaci masu harkar Cryptocurrency, matasane.   Saidai ga dukkan alama a yanzu harkar ta kare kowa da kowa na yinta. Abin tambaya anan shin gwamnatin zata fito da sabuwar dabarar hana Cryptocurrency ne ko kuwa zata ci gaba da zuba ido tunda mutane sun ki yadda su daina.
“Ba zamu iya sayar da litar man fetur kasa da naira 180 ba”>>kungiyar ‘yan kasuwar man fetur, IPMAN

“Ba zamu iya sayar da litar man fetur kasa da naira 180 ba”>>kungiyar ‘yan kasuwar man fetur, IPMAN

Kasuwanci
Kungiyar 'yan kasuwar mai ta IPMAN ta Najeriya ta bayyana cewa memboninta ba zasu iya cigaba da sayar da litar man fetur a farashin 165 ba. Kuma a kwanakin bayan dama membobin kungiyar na kudu maso yamma sun bayyana cewa ba zasu iya cigaba da sayar da man a farashin da gwamnatin ta yanke masu ba. Inda shugaban kungiyar na jihar Legas, Akin Akinrinade ya tabbatar da hakan ranar litinin cewa ba zasu sayar da litar mai a kasa da naira 180 ba. Kuma ya kara da cewa ba yanjin aiki ne yasa suka kulle gidajen mai ba yanayin kasuwar ne, kuma duk wanda yasan abinda yake a harkar mai to ba zai sayar a kasa da naira 180 ba.  
Wata sabuwa: Elon Musk yayi barazanar fasa sayen Twitter

Wata sabuwa: Elon Musk yayi barazanar fasa sayen Twitter

Breaking News, Kasuwanci
Shararren mai kudin kasar Amurka dake shirin sayen Twitter, Elon Musk yayi barazar fasa sayen kafar sada zumtar. Elon Musk na shirin sayen Twitter ne a farashin dala bilyan 44, amma yanzu yana shrin fasawa saboda akwai lauje cikin nadi tsakin shi da masu kafar sada zumuntar. Inda lauyansa ya bayyana cewa masu kafar sada zumuntar sunki baiwa Musk damar duba Twitter yadda ya kamata domin akwai asusun bogi da yawa a cikinta.
Gwamnati na shigo da Zuma ta Biliyan 2 Najeriya daga kasashen waje duk shekara

Gwamnati na shigo da Zuma ta Biliyan 2 Najeriya daga kasashen waje duk shekara

Kasuwanci
The Federal Government is spending at least $2 billion on the importation of honey yearly, while the country’s national consumption of the commodity stood at 400,000 tonnes, an animal scientist, Kingsley Nwaogu, has disclosed. Nwaogu made the assertion during a virtual lecture in Abuja while explaining that there was a growing demand for organic honey, especially by operators in the cosmetics, medicine, confectionery and the pharmaceutical industries in Nigeria. He added that our honey production is less than 40,000 tonnes (less than 10 per cent of demand), and this trend indicates a large business opportunity as it is a non-capital intensive profitable business. “Organic honey market analysis indicates that global demands for honey are projected to exceed 2.8 ...