fbpx
Monday, October 25
Shadow

Nishaɗi

Kalli Bidiyo da hotunan casun da akayi a Saudiyya kamar a Amurka da suka jawo cece-kuce

Kalli Bidiyo da hotunan casun da akayi a Saudiyya kamar a Amurka da suka jawo cece-kuce

Nishaɗi
Wani bidiyo da ya nuna mata da maza sanye da kayan ninkaya suna cashewa a bakin ruwan Jeddah ya haifar da ce-ce-ku-ce a Saudiyya. Wasu ƴan ƙasar sun fito shafukan sada zumunta suna yin Allah wadai da bidiyon wanda kamfanin dillacin labarai na AFP ya yaɗa, yayin da wasu kuma ke ganin sauyi ne aka samu. Bidiyon ya nuna maza da mata suna rawa, wasu mazan ba riga, yayin da mata kuma suke sanye da tufafi ke bai rufe jikinsu ba. https://twitter.com/aliShihabi/status/1450921291813376001?t=ARtJGn7pEt5Dlfqvp7FLCQ&s=19 A Saudiyya ba a saba ganin cuɗanyar mata da maza ba, amma bayan shekaru huɗu, yanzu abubuwa sun sauya. Sauye-sauyen gwamnatin Saudiyya yanzu ya ba matan ƙasar damar sanya kayan ninkaya da yin casu a bakin teku a Jeddah, wani abin da ake ganin s...
Adam A. Zango ya sha Alwashin yin Hidima da dukiyarsa saboda zuwa Watan Maulidi

Adam A. Zango ya sha Alwashin yin Hidima da dukiyarsa saboda zuwa Watan Maulidi

Nishaɗi
Watan Mauludi Yazo Domin haka dole mu nuna Jin dadinmu, muyiwa Bayin Allah Hidima da Dukiyarmu Albarkacin Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad S.A.W, Cewar Adam A Zango.. Shahararre Dan Wasan Hausan jarumi Adam A Zango Ya saki Wata Bidiyo Wacce ya Nuna Falala da Kuma Darajar Annabi Muhammad. Adamu zango Yace Yana mamaki Yadda Mutane ke kashewa Kansu Kuɗi Sunayin Birthday nasu tare da Nuna murnarsu , Amman Sai Kan Fiyayyen Halitta Shine ya Zama Bidi'a, Allah Ya sawake mudai Sai Munyi.. Allah Kabarmu da Manzon Allah , Kasamu cikin Cetonsa Aranar kiyama.. - Katsina Online - 08/10/2021
Da Duminsa:Jarumin Fina-finan Hausa ya rasu

Da Duminsa:Jarumin Fina-finan Hausa ya rasu

Nishaɗi
Rahotannin da BBC ke samu na tabbatar da rasuwar tauraron fina-finan Hausa na Kannywood Ahmad Tage. Kafin rasuwarsa ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya, har ta kai ga an kwantar da shi a asibitin Nasarawa da ke jihar Kano. Tuni 'yan wasan Hausa na Kannywood suka fara mika ta'aziyyarsu a shafukan sada zumunta. Ya fi fitowa a fina-finan barkwanci a tsawon lokacin da ya kwashe a harkar, wadda ya fara a matsayin mai daukar bidiyo, kafin daga bisani ya rikide ya zama tauraro. 'Yan uwansa sun shaida wa BBC Hausa cewa ya rasu ya bar mata biyu da 'ya'ya 21.
Fati Muhammad na neman Mijin aure

Fati Muhammad na neman Mijin aure

Nishaɗi
TANA NEMAN MIJIN AURE Kamar yadda kamfanin jaridar Dokin Karfe TV suka ruwaito labarin, tsohuwar tauraruwa a masana'antar Hausa film wanda aka fara da ita tun farko wato Fati Muhammad, ta fito tana shelantawa duniya cewa tana neman mijin aure Fati tace: "Na shirya tsaf ina neman miji na gari domin nayi aure" Wannan shine karshen kyawawan matan da suka sadaukar da kyawun surarsu a aikin banza, tun lokacin da suke da jini a jika ake musu nasiha su watsar da wannan sana'ar banza suyi aure amma basa yi, saboda duniya tana musu huduba Wannan babban darasi ne ga duk wata yarinya mai gigiwa da taurin kai wacce taki yin aure ta kama sana'ar film, dama ance ba farkon ba karshen, ai ko ba mutuwa akwai tsufa, kamar yadda Fati ta tsufa ta dawo tana neman miji Yaa Allah Ka bawa Fati ...
Shin da gaske Maryam Yahya ta rasu? Gaskiyar Lamari

Shin da gaske Maryam Yahya ta rasu? Gaskiyar Lamari

Nishaɗi
LABARI AKAN RASUWAR MARYAM YAHAYA JARUMAR KANNYWOOD. Tin farkon satinnan mutane suke tambayata akan cewa dagaskene maryam yahaya ta rasu? To gaskiyar magana maryam yahaya bata rasuba saidai batada lafiya Wanda ayanzuhaka tana cigaba da samun lafiya sosai. Mutane kuji tsoron Allah kudaina yada labaran karya, meye ribarka idan kayi karyar cewa wani ya rasu? Shin karyar dakayi ita zatasa ya mutu da wuri, kokuma ita zata hanashi mutuwa? Kawai kubari sai lokaci yayi sannan kuyi posting bawai kana zaune acikin dakinka kawai ka kirkire labariba. Tabbas maryam yahaya zata mutu, ni danake rubutunnan zan mutu, masu karantawa zasu mutu, masu yada labaran karya duka zasu mutu, Allah ne kawai bazai mutuba dominshi rayayyene na har abada. Allah yakarawa maryam yahaya lafiya da Nis...
Da Duminsa: Fadan Ummi Rahab da Adam A. Zango yayi kamari, Ummi ta kai magana gaban hukuma

Da Duminsa: Fadan Ummi Rahab da Adam A. Zango yayi kamari, Ummi ta kai magana gaban hukuma

Nishaɗi
Ga dukkan Alamu ba'a gama jin bayanai ba kan rashin jituwar da ke tsakanin Ummi Rahab da Adam A. Zango ba.   A wani sabon rahoto, da muka samu, Ummi Rahab ta kai magana gaban hukuma inda tace an bata mata suna.   Saidai ba'a san wa ta kai ba, shin Adam A. Zangon ko kuwa?   Ali Artwork wanda aka fi sani da Madagwal ne ya saka takardar korafin da Ummi ta mikawa hukumar 'yansandan farin kaya ta DSS.   Saidai ba'a ga cikakken bayanin da takardar ta kunsa ba. Inda Ali Artwork yawa Ummi fatan Allah ka baiwa me gaskiya gaskiyarsa.    
Ni baki bai kamani, nasha tabara na sha yasin>>Ummi Rahab

Ni baki bai kamani, nasha tabara na sha yasin>>Ummi Rahab

Nishaɗi
Matashiyar fina-finan Hausa, Ummi Rahab da labarin rabuwarta da me gidanta, Adam A. Zango ke yawo a shafukan sada zumunta ta bayyana cewa baki bai kamata.   Ta bayyana hakane a wani bidiyo da Ali Art Work ya wallafa a shafinsa inda yake cewa gaskiya zata yi halinta.   Artwork wanda aka fi sano da Madagwal ya kara da cewa gaskiya zata yi halinta akan wannan lamari kuma masu zarginsa da ba daidai ba, zasu gane gaskiya.   Saidai yace duk wanda ya zargeshi akan aikata ba daidai ba a wannan lamari, ya yafe masa.