fbpx
Thursday, April 22
Shadow

Siyasa

2023: Rashin tsaro ba zai iya hana Kudu maso Gabas samar da shugaban kasa ba – Sanata Ogba

2023: Rashin tsaro ba zai iya hana Kudu maso Gabas samar da shugaban kasa ba – Sanata Ogba

Siyasa
Sanata mai wakiltar Ebonyi ta Tsakiya, Obinna Ogba ya ce kashe-kashen baya-bayan nan da aka yi a Ebonyi da wasu jihohin kudu maso gabas ba zai hana yankin samar da Shugaban kasa na gaba ba. Mista Ogba ya fadi haka ne a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a kan kudirin da ya gabatar tun farko a zaman majalisar na ranar Laraba. A cewar Mista Ogba, rikicin ba zai iya hana su samar da shugaban kasa ba, dalili kuwa shi ne, akwai rashin tsaro a wasu sassan kasar amma ba mu dakatar da su ba daga samar da shugaban kasa ba, don haka rashin tsaro ba zai zama hujja ba na hana mu samar da shugaban kasar daga yankin mu ba. Tun da farko a cikin yunkurin nasa, Mista Ogba ya nuna damuwa game da tabarbarewar yanayin rashin tsaro a kasar wanda a cewarsa, ya yadu a mafi yawan bangarorin...
Kuma Dai: An fito da wani sabon Kazafi akan Sheikh Pantami

Kuma Dai: An fito da wani sabon Kazafi akan Sheikh Pantami

Siyasa
Baya ga zargin cewa yana goyon bayan kungiyoyin ta'addanci a shekarun baya wanda kuma ya warware lamarin a wani jawabi da yayi, an sake fito da wata sabuwar magana mara dadi da ake zargin Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Sheikh Isa Ali Pantami.   Jaridar People's gazette ta ruwaito cewa wai Sheikh Pantami a shekarun baya, ya Shirya kashe tsohon gwamnan jihar Kaduna, Patrick Ibrahim Yakowa.   Jaridar ta bayyana cewa a shekarar 2010 ne Sheikh Pantami ya jagoranci zaman taron da sauran wasu membobin kungiyar JNI. Ta wallafa wata takarda wadda ta yi ikirarin cewa itace aka cimma matsaya a wajan taron. Ta kuma bayyana cewa ta nemi jin ta bakin Minista akan wannan zargi amma bai ce komai ba.   A kwanakinnan dai an sako Ministan gaba ana ta dangantashi...
A kawo mana dauki, Sojoji nawa matasanmu kamen ba sani ba sabo>>Inyamurai

A kawo mana dauki, Sojoji nawa matasanmu kamen ba sani ba sabo>>Inyamurai

Siyasa
Wata kungiyar kare muradun Inyamurai ta koka da cewa Sojojin Najeriya nawa matasa da mata kamen ba sani ba sabo akai-akai. Kungiyar ta bayyana cewa, sojojin na kamen ne idan sika ga mutum da suke tunanin yana da alaka da kungiyar IPOB.   Sun bayyana cewa, lamarin na faruwane a Ohaji-Egbema dake karamar Hukumar Oguta.   Shugaban Kungiyar, Chilos Godsent yayi kira ga Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma da Shugaban kasa, Muhammadu Buhari su kai musu dauki.
Marasa Rinjaye na majalisar Wakilai sun so a tsige Pantami amma kakakin majalisar yaki Amincewa

Marasa Rinjaye na majalisar Wakilai sun so a tsige Pantami amma kakakin majalisar yaki Amincewa

Siyasa
Shugaban marasa Rinjaye na majalisar Wakilai, Ndudi Elumelu yayi kira ga majalisar da ta nemi a sauke Ministan sadarwa da tattalin arzikin Zamani, Sheikh Isa Ali Pantami.   Saidai kakakin majalisar, Femi Gbajabiamila bai aminta da hakan ba.   Bayan da Elumelu ya kammala bayaninsa, Femi Gbajabiamila ya gaya masa cewa ya jishi sannan kuma ya buga sandar ikonsa.
Akwai makarantu 62,000 da za’a iya kaiwa Hari a Najeriya>>Minista Kudi

Akwai makarantu 62,000 da za’a iya kaiwa Hari a Najeriya>>Minista Kudi

Siyasa, Uncategorized
Ministar Kudi, Zainab Shamsuna Ahmad ta bayyana cewa, akwai makarantu 62,000 da suke cikin hadarin kai musu hari a Najeriya.   Ta bayyana hakane ranar Talata a wajan wai taro da aka tattauna yanda za'a ciyar da makarantun Najeriya gaba a Abuja.   Zainab ta bayyan cewa zasu samar da yanayin karatu me kyau ga daliban kuma zasu hada hannun da bangaren masu zaman kansu dan dan cimma wannan manufa. “62,000 schools are physically porous and this is a very large number. This is not to say that building a fence actually stops abductions. “We must also educate children, teachers and communities and put alarm systems in place. Like the head of civil defence says, educate the communities to know what to expect and identify telltale signs of abduction. “We will come ...
EFCC sun Tsare tsohon Gwamnan Zamfara, Yari

EFCC sun Tsare tsohon Gwamnan Zamfara, Yari

Siyasa
Hukumar yaki da Rashawa da cin hanci, EFCC ta tsare tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari a jiya, Talata.   Lamarin ya farune a Ofishin hukumar dake Sokoto.   An tsare Yari ne bisa zargin almundahanar wasu makudan kudi. Wata majiya daga hukumar EFCC ta bayyanawa Daily Trust cewa akwai yiyuwar a tsare tsohon gwamnan har nan da mako 1.
Ku binciki Pantami>>Kungiyar Kiristoci ta CAN ta gayawa DSS

Ku binciki Pantami>>Kungiyar Kiristoci ta CAN ta gayawa DSS

Siyasa
Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN, watau Rev. Samson Ayokunle ya bayyanawa hukumar 'yansandan farin kaya ta DSS cewa, su binciki ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Sheikh Isa Ali Pantami.   Da yakw magana a wajan taron cocin da aka yi a Ibadan, Samson ya bayyana cewa, shin wai me DSS suke yi?   Yace wanna ba abune da za'a daukeshi sakwa-sakwa ba. Saidai da aka tambayeshi konme yasa DSS din basu Binciki Pantami ba, ya bayyana cewa bai sa Dalili ba. “What is the State Security Service doing? What are the police doing? What is the Director-General of the National Intelligence Agency doing about the allegation? Such allegations should not be taken with levity. It should be taken seriously especially if we have data, written evidence, implicating ...
Najeriya zata dawo da Jakadiyarta ta kasar Ingila saboda baiwa ‘yan IPOB Mafaka

Najeriya zata dawo da Jakadiyarta ta kasar Ingila saboda baiwa ‘yan IPOB Mafaka

Siyasa
Akwai yiyuwar Gwamnatin tarayya ta dawo da jakadiyarta ta kasar Ingila saboda yanda kasar ta baiwa tsageran IPOB mafaka.   Kasar Ingila ta baiwa tsageran IPOB da gwamnati ke takurawa damar neman mafaka a kasarta. Hakan ya batawa gwamnatin Najeriya rai sosai inda Ministan Yada Labarai da Al'adu, Lai Muhammad ya bayyana hakan da yiwa yaki da Ta'addanci n da Najeriya ta ke zagon kasa.   'Yan IPOB dai na fafutukar ganin an baiwa Inyamurai kasarsu. Saidai ana zarginsu da kaiwa jami'an tsaro hare-hare.
Majalisar Tarayya na Shirin amincewa da kafa ma’aikatar kula da dabbobi

Majalisar Tarayya na Shirin amincewa da kafa ma’aikatar kula da dabbobi

Siyasa
Rahotanni sun bayyana cewa, Majalisar Dattijai na shirin amincewa da kafa wata hukuma da zata rika kula da dabbobi.   Kudirin dokar dan majalisa, Birma Muhammad Enagi ne ya kaishi zauren majalisar inda kuma tuni ya tsallake karatu na 2.   Dan majalisar yace idan aka kafa wannan hukuma, zata taimaka wajan hana yawo da dabbobi n zuwa guri-guri kuka zai taimaka wajan rage yawan satar Shanin.