
Wani kauye a Zamfara ya biya miliyan 5 dan a baiwa ‘yansanda su karesu daga hare-haren ‘yan Bindiga
Kauyen 'yar Katsina dake jihar Zamfara ya bayar da Miliyan 5 dan a baiwa 'yansanda su samar musu da tsaro a garin nasu.
Saidai da bincike yayi tsanani, an gano cewa, wasu ne suka damfari kauyawan suka marbi kudin.
Hukumar 'yansandan da aka kai kauyenne suka kama wadanda suka karbi wannan kudi.
Mutanen kauyenne suka kai karar mutanen kamar yanda jami'in hukumar, SP Muhammad Shehu ya bayyana.