fbpx
Monday, November 29
Shadow

Uncategorized

Bidiyon kwallon da Jadon Sancho ya ciwa Manchester United

Bidiyon kwallon da Jadon Sancho ya ciwa Manchester United

Uncategorized
Tauraron dan kwallon Manchester United,  Jadon Sancho ya ci kwallonsa ta 2 a kungiyar Manchester United tun bayan komawarsa kungiyar daga Borussia Dortmund.   Ya ci kwallonsa ta biyunne a wasan da suka buga da Chelsea da yammacin jiya. https://twitter.com/UtdDistrict/status/1465079253356224525?t=P3MmJY_j2354532g-T-Fyg&s=19 Saidai Chelsea ta farke kwallon ta hannun Jorginho da bugun daga kai sai me tsaron raga.
Bai kamata kana hadamu da ‘yan ta’adda ba>>IPOB ga Sheikh Gumi

Bai kamata kana hadamu da ‘yan ta’adda ba>>IPOB ga Sheikh Gumi

Uncategorized
Haramtacciyar kungiyar dake neman kafa kasar Biafra,  IPOB ta caccaki babban malamin addinin Islama, Sheikh Gumi inda ta bayyana cewa bai kamata yanda yake hadasu da 'yan ta'adda ba.   Kakakin kungiyar, Emma Powerful ne ya bayyana haka a sanarwar da ya fitar ga manema labarai.   Yace IPOB tana kasashe sama da 100 a Duniya kuma babu inda ake kiranta da sunan 'yan ta'adda sai a Najeriya.   Kungiyar ta kara da cewa, ya kamata Sheikh Gumi ya boye fuskarsa cikin kunya saboda yanda yake goyon bayan masu kisan mutane.   Tace a baya ana ganin girman malamin amma a yanzi ya zubar da kimarsa.
Ya kamata a rika barin ‘yan Najeriya masu hankali na mallakar Bindiga>>Jigo a APC

Ya kamata a rika barin ‘yan Najeriya masu hankali na mallakar Bindiga>>Jigo a APC

Tsaro, Uncategorized
Jigo a jam'iyyar APC, Chief Ben Adaji ya nemi cewa a rika barin 'yan Najeriya masu hankali na mallakar Bindiga.   Ya baia shugaban 'yansanda shawarar cewa kamata yayi a baiwa mutane masu hankali lasisin rike Bindiga saboda kariyar kai.   Ya bayyana hakane ga manema labarai a jalingo inda yace yanda 'yan Najeriya da basu ji ba basu gani ba ke fama da fargaba saboda matsalar tsaro abin damuwa ne.   Ya bayar da shawarar cewa bai kamata a harwa jami'an tsaro kadai harkar samar da tsaro ba.
Ya kamata duk Wanda aka kama yawa diyarsa fyade a rika dandakesu>>Ministar Mata

Ya kamata duk Wanda aka kama yawa diyarsa fyade a rika dandakesu>>Ministar Mata

Uncategorized
Ministar mata Paulin Tallen ta bada shawarar a rika hukuncin dandake duk wani da aka samu yawa diyarsa fyade.   Ta bayyana hakane a wajan wani ganawa da manema labarai ranar Lahadi a Abuja wanda ya mayar da hankali kan yaki da cin zarafin da akewa mata.   Ta bayyana masuwa 'ya'yansu mata fyade a matsayin mafi munin cin zarafi wanda tace ya kamata a rika daukar tsatstsauran mataki akan irin wannan abu.   Ta yi kira ga 'yan jarida su rika yayata sakon yaki da cin zarafin mata a tsakanin al'umma. “Incest is the worst form of gender based violence and I advocate castration as punishment for offenders. ‘Let us name and shame the perpetrators of incest because it is the worst,” she said    
A matsayina na shiru-shiru da baison shiga jama’a bai kamata in shiga siyasa ba>>Jonathan

A matsayina na shiru-shiru da baison shiga jama’a bai kamata in shiga siyasa ba>>Jonathan

Uncategorized
Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya bayyana cewa, a matsayinsa na wanda baison shiga jama'a bai kamata ace ya shiga siyasa ba.   Jonathan ya bayyana hakane a ganawarsa da 'yan makarantarsu na jami'ar Fatakwal da suka yi karatu tare.   Yace yana kokarin ganin ya gano kodai ya shiga siyasa ne bagatatan ba tare da ya shirya ba?   An kwashe kwanaki 3 ana taro tsakanin Jonathan din da abokan ajinsu. Ya bayyana cewa, shiga siyasa na tattare da wata kalar rayuwa ta daban da ba lallaj ne kowa ya iya yadda da hakan ba.
An Gudunar Da Zanga-zanga a Wasu Unguwannin Garin Bauchi

An Gudunar Da Zanga-zanga a Wasu Unguwannin Garin Bauchi

Siyasa, Uncategorized
Al’umomin Unguwar Tirwun da na sashen rukunan Jamiar Abubakar Tafawa Balewa a wajen Birnin Bauchi, sun gudanar da zanga zanga da kuma datse babbar hanyar data wuce Maiduguri,a wani mataki na kin amincewa da assasa Kamfanin tara iskar gas da Kamfanin mai suna Action Energy ke yunkurin ginawa. Bincike ya nuna wurin da ake son kafa cibiyar tara iskar gas din, yana cikin rukunan mazaunin al’umma ne ba kamar yadda gwamnatin Jihar Bauchi ta tsara ba, da aka kebe wuri na musamman domin kamfanonin ya dangin wadannan. Masu zanga zangar da ya hada har da maza da mata suna zargin mutumin dake son samar da matattarar Iskar gas din da yin watsi da umurnin da hukumomi suka bashi na tsaida aikin gina matattarar iskar gas din bisa la’akari da irin barazanar da zai iya faruwa. idan aka samu fashe...