fbpx
Friday, August 19
Shadow

Wasanni

Manchester United zata dauki Casemiro daga Real Madrid

Manchester United zata dauki Casemiro daga Real Madrid

Wasanni
Kungiyar Manchester United na shirin daukar tauraron dan wasan tsakiya na kungiyar Real Madrid, Casemiro. Dan wasan ya sabunta kwantirakinsa da Madrid ne a shekarar data gabata izuwa shekarar 2025 kuma ta saka masa farashin yuro biliyan guda. Amma Manchester Uniteda ta taya sane a farashin yuro miliyan 60 kuma tana fatan dan wasan zai amince ya koma kungiyar. Manchester United na shan suka a wannan kakar biyo bayan kashin data sha a wasanni biyu data buga na bana, kuma itace a kasan teburin gasar ta firimiya.
Da Dumi Duminsa: Elon Musk zai saya kungiyar Manchester United

Da Dumi Duminsa: Elon Musk zai saya kungiyar Manchester United

Breaking News, Wasanni
Shahararren mai kudin duniya wanda ke tsaka mai wuya da kafar sada zumunta ta Twitter kan fasa sayenta daya yi, Elon Musk ya bayyana cewa zai saya kungiyar Ingila ta Manchester United. Elon Musk babu shakka zai iya sayen kungiyar gasar firimiyar domin kudinsa ya kai dala biliyan 260 kuma ita farashin kungiyar dala biliyan biyu ne a cewar rahotanni, Yayin da kuma mujallar Forbes ta bayyana cewa farashinta dala biliyan 4.6 ne kuma a shekarar data gabata kungiyar ta samu dala miliyan 633 kudin shiga. Kungiyar Manchester United itace a kasan teburin gasar firimiya biyo bayan shan kashin data yi a wasanni biyu data fara bugawa na bana.  
‘Yan wasan Manchester sun bukaci a sayar da Ronaldo kuma har yanzu baya jituwa da sabon kocin kungiyar

‘Yan wasan Manchester sun bukaci a sayar da Ronaldo kuma har yanzu baya jituwa da sabon kocin kungiyar

Wasanni
Tauraron dan wasan Manchester United na gaba Cristiano Ronaldo har yanzu baya jituwa da sabon kocin kungiyar, Erik Ten Hag. A baya dan wasan Portugal din ya bukaci Manchester ta sayar dashi a wannan kakar domin ya buga gasar zakarun nahiyar turai, amma babu kungiyar dake nemansa. Kuma yana cikin tawagar United data sha kashi daci hudu bako daya a hannun Brentford, yayin da bayan an tashi wasan mataimakin kocin Steve ya bukaci Ronaldo ya sanyaya ran masoyansu amma yaki. Kuma halayyar da dan wasan keyi ta fara shafar sauran 'yan tewagar wanda hakan yasa wasu sukace kawai a barshi ya sauya sheka su huta.
Liverpool tasha da kyar a hannun Palace sun tashi wasa da kunnen doki bayan Nunez ya samu jan kati

Liverpool tasha da kyar a hannun Palace sun tashi wasa da kunnen doki bayan Nunez ya samu jan kati

Wasanni
Kingiyar Liverpool ta sake raba maki a wasanta na biyu a wannan kakar baya sun tashi wasa da kunnen doki 1-1 tsakaninsu da Crystal Palace. Wilfried Zaha ne ya fara ciwa Crystal Palace kwallo a wasan tun kafin aje hutun rabin lokaci a minti na 34. Kuma bayan an dawo daga hutun rabin lokaci zakaran gwajin Liverpool Darwin Nunez ya samu jan kati a minti na 57 wanda hakan yasa kungiyar ta samu babban cikas a wasan. Amma sai dai Luiz Diaz ya taimakawa tawagar ta Jurgen Klopp ta tsira da maki guda wanda hakan yasa ta gujewa shan kashi a gida karo na farko tun shekarar 2017.
Koulibaly ya haskaka yayin da Chelsea ta raba maki da Tottemham bayan sun tashi wasa da kunnem doki 2-2

Koulibaly ya haskaka yayin da Chelsea ta raba maki da Tottemham bayan sun tashi wasa da kunnem doki 2-2

Uncategorized, Wasanni
Kungiyar Tottenham da Chelsea sun tashi wasa da kunnen doki a wasan da suka buga na gasar firimiya a yau ranar lahadi 14 ga watan Augusta. Chelsea ce ta fara jagoranci a wasan inda kwalliya ta biya kudin sabulu domin sabon dan wasan baya data dakko daga Napoli, Kalidou Koulibaly ne yaci mata kwallon. Kafin Højbjerg ya ramawa Tottenham kwallon sannan Reece James ya kara ciwa Chelsea guda. Duk da haka dai a karshe raba maki sukayi domin zakaran gwajin Spurs Harry Kane saida ya kara ciwa tawagar Antonio Conte kwallo guda.
Yadda Sadio Mane yaci kwallaye biyu aka soke a wasan da Munich ta lallasa Wolfsburg daci 2-0

Yadda Sadio Mane yaci kwallaye biyu aka soke a wasan da Munich ta lallasa Wolfsburg daci 2-0

Breaking News, Wasanni
Kungiyar zakarun gasar Bundesliga ta lallasa Wolfsburg daci biyu bako daya duk da cewa an soke mata kwallaye uku data ci a wasan. Jamal Musaila ne ya fara ciwa Munich kwallo ta farko kafin Kimmich ya taimakawa Muller ya kara zirawa masu kwallo ta biyu a wasan. Yayin da kungiyar ke cigaba da samun masara a wasanninta duk da cewa zakaran gwajinta Robert Lewandowski ya sauya sheka ya koma Barca a wannan kakar. Kuma sabon dan wasan data dakko daga Liverpool, Sadio Mane yaci mata kwallaye biyu amma an soke, inda Upamecano shima yaci kwallo wadda itama dai aka soke.
Neymar na haskakawa a wannan kakar biyo bayan kwallaye biyu daya ciwa PSG a wasanta da Montpellier

Neymar na haskakawa a wannan kakar biyo bayan kwallaye biyu daya ciwa PSG a wasanta da Montpellier

Breaking News, Wasanni
Tauraron da dan wasan gaba na kungiyar Paris Saint Germain, Neymar na cigaba da haskakawa a wannan kakar bayan daya ciwa kungiyar kwallaye biyu a wasanta da Montpellier. Paris Saint Germain 5-2 ta lallasa Montpellier a wasan duk da cewa Mbappe ya barar mata da bugun daga kai sai mai tsaron raga, Amma dan wasan Faransan ya wanke kansa domin yaci mata kwallo guda a wasan, wanda hakan yasa yanzu PSG taci wasanni uku data buga na bana. Kuma shima sabon kocinta Christophe Galtier ya fara horas da kungiyar da kafar dama domin kwallaye 14 PSG ta zira a wasanni ukun.
Kuyi hakuri laifi na ne, cewar mai tsaron ragar United bayan tasha kashi daci 4-0 a hannun Brentford

Kuyi hakuri laifi na ne, cewar mai tsaron ragar United bayan tasha kashi daci 4-0 a hannun Brentford

Breaking News, Wasanni
Kungiyar Manchester United tasha kashi daci daci hudu bako daya a hannun Brentford, wanda hakan yasa ta fadi gabadaya wasanni biyu data buga na bana. Tun kafin aje hutun rabin lokaci ne Brentford ta lallasa United daci hudun ta hannunn Dasilva, M. Jensen, B. Mee, da kuma B. Mbeumo. Wanda hakan yasa Brentford ta zamo kungiya ta uku data lallasa United daci hudu tun kafin aje hutun rabin lokaci, Bayan Liverpool da Tottenham wanda sune kadai suka taba yiwa Manchester United wannan lallasar. Kuma bayan an tashi wasan mai tsaron ragar United, David De Ge ya bayar da hakuri inda yace laifin sane lallasar da suka sha a hannun Brentford.
Manchester ta cigaba da tsare kofinta na firmiya, inda ta lallasa Bournemouth daci 4-0

Manchester ta cigaba da tsare kofinta na firmiya, inda ta lallasa Bournemouth daci 4-0

Breaking News, Uncategorized, Wasanni
Kungiyar Manchester City ta cigaba da buga wannan kakar da kafar dama bayan data lallasa Bournemouth daci hudu bako daya. City tayi nasarar cin kwallayen nata ne ta hannun Gundogan, Kevin De Bruyne, Phil Foden sai kuma dan wasan Bournemouth ya kara mata kwallo guda waro Larma ana daf da tashi wasa. Inda ta cigaba da tsare kofinta na gasar data lashe a kakar data gabata bayan data ci gabadaya wasanni biyu data buga a wannan kakar.  
Jesus ya fara bugawa Arsenal wasa da kafar dama inda yaci mata kwallaye biyu ta lallasa Lecester City 4-2

Jesus ya fara bugawa Arsenal wasa da kafar dama inda yaci mata kwallaye biyu ta lallasa Lecester City 4-2

Breaking News, Uncategorized, Wasanni
Arsenal tayi nasara a wasa na biyu data buga a wannan kakar biyo bayan ta lallasa Leicester City daci hudu da daya. Sabon dan wasan data dakko daga Manchester City, wato Gabriel Jesus ne yaci mata kwallaye biyu tun kafin aje hutun rabin lokaci. Kuma bayan dawo Granit Xhaka da Martinelli suka kara ci mata kwallaye biyu sai William Saliba yayi kuskuren ciwa Leicester City kwalli guda, Inda shima James Maddison ya kara ciwa Leicester City kwallo guda aka tashi wasan Arsenal nacin 4-2.