fbpx
Saturday, December 4
Shadow

Charles Soludo na APGA ya zama gwamnan jihar Anambra

A Najeriya, hukumar zaben kasar ta bayyana Farfesa Charles Chukuma Soludo na jam`iyyar APGA a matsayin sabon gwamnan jihar Anambra.

Shugabar jami’ar Calabar, wadda ita ce kuma mai bayyana sakamakon zaben, Farfesa Florence Obi ta sanar da sakamakon da cikin dare da misalin karfe biyu saura minti goma, inda ta ce Soludon ya samu kuri’a 112,229.

Sai kuma Valentine Ozigbo na jam’iyyar PDP wanda ya zo na biyu da yawn kuri’a 53,807.

A ranar Asabar ne aka gudanar da zaben gwamnan a jihar Anambra, inda ‘yan takara goma sha takwas suka fafata a zaben.

Matsalar tsaro ta janyo ba a yi zabe a karamar hukuma daya daga cikin 21 da ake da su a jihar ba.

Inda hukumar zaben ta dakatar da sanar da sakamakon, har sai da aka sake zabe a karamar hukumar Ihiala a ranar Talata.

To wanene Charles Soludo?

An haifi Farfesa Charles Chukwuma Soludo ne a ranar 28 ga watan Yuli, 1960, a Ƙaramar Hukumar Aguata ta Jihar Anambra.

Ya yi digirinsa na farko da na biyu da kuma digirin digirgir duka a fannin tattalin arziki. Sannan ya samu horo a wasu manyan cibiyoyi na duniya, ciki har da: Cibiyar Brookings da ke Washington, DC; da Jami’ar Cambridge da ke Birtaniya da kuma Jami’ar Oxford.

Sabon gwamnan jihar ta Anambra, Farfesa Charles Chukwuma Soludo ya shafe shekara biyar a matsayin Gwamnan Babban Bankin Najeriya. Sai kuma bankin duniya da kuma wadansu manyan hukumomi na duniya, ciki har da hukumar bayar da lamuni ta duniya, IMF. Kuma ya samu nasara mai yawa da tarin lambobin yabo.

Za a iya cewa Farfesa Soludo ba kyallen yadawa ne idan aka yi la`akari da irin kwarewarsa a fannin tattalin arziki ba.

Amma a fannin mulki, masana na ganin cewa sai sabon gwamnan ya hada da dabaru irin na siyasa saboda aikin da ke gabansa ba karami ba ne.

Farfesa Jibrin Ibrahim masanin siyasa a Najeriya ya ce daya daga cikin kalubalen da ke gabanshi, shi ne na masu neman ‘yancin Biafra, saboda a cikin kowanne mako suna ware ranaku biyu su hana mutane fita.

Wani abun kuma shi ne sabon gwamnan zai ga babu kudi na tafiyar da ayyukan gwamnati.

Sannan kudaden shiga ba shigowa suke yi sosai kamar lokutan baya ba, musamman ganin ‘yan kasuwa ba sa samun damar fitowa gudanar da kasuwancinsu, don haka tafiyar da mulkin ba zai zo ma sa da sauki ba.

”watakila sabon gwamnan zai iya amfani da wannan dama wajen nuna wa mutanen jihar cewa babu abin da zai samu matukar ba a zauna lafiya ba, a wannan lokacin ne ita ma gwamnati za ta iya gudanar da aikinta.”

Shugabanni da manyan mutanen da suka fito daga shiyyar kudu-maso gabashin Najeriyar da dama na dari-dari ko já-baya wajen fuskantar matasan da ke wannan fafutuka ta ballewa daga Najeriya gudun irin martanin da suke yi na hare-hare.

Amma Farfesa Jibrin Ibrahim ya ce ranar wanka ba a boyon cibi, don haka wajibi ne sabon gwamnan da takwarorinsa su fito baro-baro su fada wa juna gaskiya, cewa `yan kabilar Igbo da Najeriya tamkar sabar kafar kaza ne, wato mutu ka raba!

”Mutanen nan babu jihar da ba sa ciki a Najeriya, sun yi kudi sun gina gidaje, su ke kasuwanci don haka ba zai yiwu a ce duka su koma gida su yi Biafra ba, domin kasar ma ba za ta ishe su ba.

Don haka dole su fara fitowa suna nuna wa mutanen da ke neman Biafra cewa ba abu ne da zai sa su samu zaman lafiya da samun arzikin da suke samu daga jihohin da ke kasar nan ba.

Dole su cire tsoro su fada wa yaran nan gaskiya, su fada musamman abin da suke so ba zai samu ba,” in ji Farfesa Jibrin.

Wani aikin da ke gaban sabon gwamnan, kamar yadda masana ke cewa shi ne batun hada kan al`ummar jihar, musamman ma sauran abokan hamayyarsa mutum 17 da aka fafata da su a zaben da kuma jama`arsu, wadanda masana ke cewa kowanne na ji da kansa da saboda yana da farcen-susa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *