fbpx
Tuesday, August 3
Shadow

China ta gargaɗi Kasashen Turawa: ‘Lokaci ya wuce da za ku dinga juya duniya’

China ta gargaɗi ƙungiyar G7 ta ƙasashe mafiya girman tattalin arziki cewa lokaci ya wuce da wani “ƙaramin rukunin” ƙasashe zai dinga bai wa duniya umarni.

Kalaman na jakadan China a Birtaniya na zuwa ne yayin da shugabannin da ke taro a ƙasar suka nemi a haɗa kai domin tunkarar manufofin China.

Shugabannin sun zayyana kuɗaɗen da za su kashe domin daƙile take-taken China a faɗin duniya.

Masana na ganin cewa Shugaban Amurka Joe Biden da gaske yake wajen ganin shugabannin Turai sun ɗauki mataki kan China.

A yau Lahadi ake sa ran shugabannin za su sanar da ƙarin tallafi ga ƙasashe masu tasowa da ke fama da matsalolin sauyin yanayi, da kuma kuɗaɗen gudanar da ayyukan more rayuwa a matsayin kishiyar wanda Chinar ke gudanarwa.

“Mun yi imani cewa ƙasashe komai girma ko ƙanƙantarsu, ƙarfi ko gazawarsu, arziki ko talaucinsu, duka ɗaya ne,” kamar yadda Reuters ya ruwaito kakakin ofishin jakadancin China a Landan yana faɗa.

“Haka nan, ƙasashe ne baki ɗayansu ya kamata su tattauna makomar al’amuran duniya ta hanyar tuntuɓa,” in ji shi.

BBChausa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *