fbpx
Monday, May 10
Shadow

Cikin jama’ar jihar Ondo ya duri ruwa yayin da Fulani da yawa suka shiga jihar

Jama’ar Jihar Ondo dake yankun Okitipupa sun razana bayan da Fulani da yawa suka shiga yankin nasu.

 

Sun bayyana cewa sun ga Fulani akalla 45 a yankun nasu.

 

Rahoton ya bayyana cewa a ranar Alhamis ne da dare misalin karfe 9 aka sauke Fulanin a yankin ba tare da sanin dalilin yin hakan ba, shuwagabannin yankin dai sun garzaya wajan hukumar Amotekun suka sanar da ita.

 

An dai yi gaggawar tare Fulanin aka hasu Shiga cikin garin inda aka mikasu ga hukuma dan bincike, kamar yanda Vangauard ta ruwaito.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *