fbpx
Monday, November 29
Shadow

Cire tallafin man fetur zai kara jefa talakan Najeriya cikin tasku>>Sanata Shehu Sani

Ƴan Najeriya na ci gaba da bayyana fargaba da tababa kan makomarsu muddin cire tallafin man fetur baki ɗaya ya kankama nan da wasu ‘yan watanni.

Tun bayan samun sanarwar daga gwamnatin ƙasar da ke tabbatar da cewa a watannin farkon shekara mai kamawa ta 2022 za a cire tallafin mai baki ɗaya ake ta tafka muhawara da ce-ce-ku-ce.

Gwamnati dai a ta bakin, Ministar Kuɗi, Zainab Ahmed ta ce gwamnati ba ta sanya tallafin man fetur da lantarki cikin tsare-tsaren kuɗinta na 2022.

Sannan ta shaida cewa a maimakon tallafin mai za a koma bai wa ‘yan Najeriya masu karamin karfi tallafin sufuri na naira dubu biyar-biyar a kowanne wata.

Sai dai cikin masu tsokaci kan wannan mataki na gwmanati, kamar tsohon Sanata Shehu Sani ya ce wannan yunkuri zai sake tabarbare lamura da ta’azzara tsadar rayuwa a Najeriya.

Sanata Shehu Sani ya nuna rashin gamsuwarsa da tsarin raba wa talaka nair dubu biyar kowanne wata da sunan rage radadin cire tallafin mai.

Sanata ya kare hujjarsa da cewa a Najeriya yanzu naira dubu biyar ba za ta saya wa mutum abin kirki ba ko biyan haya ko sayen abinci.

Ya ce tsarin gwamnati na kare manufarta da sunan samun kudaden yi wa talaka aiki, amma a zahiri karshenta kudaden a karkatar da su maimakon ayyukan cigaban kasa.

Sannan sanatan ya tabo batun kudaden bashi da ake karba a kullum yana mai cewa har yanzu babu wani sauyi in ban da karin matsalolin kan ‘yan kasa.

“Galibi karshenta kudin tallafin da aka cire a karkatar da kudade musamman a Najeriyar wannan zamanin.

“Akwai tarin yaudara kan yadda ake tafiyar da lamuran Najeriya, saboda a kullum ana ranto kudaden bashi amma babu wani sauyi.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *