fbpx
Wednesday, May 12
Shadow

Coronavirus: Babu tabbas kan gudanar da aikin hajji a bana

Ma’aikatar aikin hajji da Umra ta kasar saudiyya ta nemi kasashen duniya da su dakata da karbar kudaden jama’a domin zuwa aikin hajjin bana, har zuwa lokacin da al’amura suka daidaita.

A wani sako da ministan ma’aikatar ya wallafa a shafinsa na Twitter, ma’aikatar ta ce yanke hukuncin aikin hajji yanzu zai zamo aikin gaggawa, inda ya nemi da a kara tsahirtawa a ga abin da zai je ya zo dangane da cutar coronavirus.

ta kuma kara da cewa Saudiyya ta mayar wa da duk mutumin da ya biya kudin bizar Umrar bana kudadensu.

Ma’aikatar aikin hajjin ta kara da cewa mutanen da suka makale a Makka sakamakon dokar kunle a kasashensu za a tsugunar da su a otal na alfarma da kulawa ta musamman har zuwa lokacin da kasashensu za su bude kofa.

Sai dai ma’aikatar ta fadi dalilin barin mutane kalilan su yi dawafi, inda ya ce sun dauki hukuncin ne saboda yin ragakafi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *