fbpx
Wednesday, May 12
Shadow

Coronavirus: Gwamnatin jihar Kano ta umarci ma’aikatanta su koma bakin aiki

Gwamnatin jihar Kano ta umarci ma’aikatan gwamnatin jihar su koma aiki.

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar laraba.

Malam Garba ya bayyana cewa an ɗauki matakin ne bayan nasarar da aka samu a yaki da annobar cutar korona a watanni ukun da suka gabata.

Haka kuma kwamishinan ya ce dole ne shugabannin hukumomi da manyan jami’an gwamnati su tabbatar an bi umarnin da gwamnatin ta fitar a hukumominsu.

Dama dai tun a watan Janairun wannan shekarar ne gwamnatin jihar Kano ta buƙaci ma’aikatanta su zauna a gida bayan da cutar korona ta fara ƙara yaɗuwa a jihar.

BBChausa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *