fbpx
Thursday, May 6
Shadow

Coronavirus ta lakume rayuka fiye da dubu 170

Kididdiga ta nuna cewa adadin mutanen da annobar coronavirus ta hallaka a kasashe 193 da ta fantsama tun bayan bullarta a China cikin watan Disamban bara, yanzu ya zarta dubu 170, yayin da cutar ta kama mutane sama da milyan 2 da rabi a sassan duniya.

 

 

Kasar Amurka na kan gaba wajen samun mamata a duniya, inda ta rasa mutane sama da dubu 40 bayan kamuwa da annobar.

 

 

Hukumomin kiwon lafiya na duniya na ci gaba da gargadin gwamnatocin kasashen duniya ciki har da Amurka da ke shirin sassauta dokar takaita zirga-zirga wadda suka kafa da zummar shawo kan wannan annoba.

 

 

A cewar masa kiwon lafiyar, har yanzu ba a ci galabar annobar COVID-19 ba, lura da yadda take ci gaba da lakume rayuka babu kakkautawa tare da yaduwa cikin sauri.

Da dama daga cikin kasashen duniya da suka kafa dokar hana fita, na kokawa kan illar da matakin ya haifar wa tattalin arzikinsu, lamarin da ya sa suke fatan gaggauta janye dokar domin fara fuskantar habbaka tattalin arzikin da ya durkushe a sanadiyar coronavirus.

 

 

Fiye da rabin al’ummar duniya aka killace a gidajensu domin hana yaduwar annobar coronavirus.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *