fbpx
Sunday, September 19
Shadow

Coronavirus zagaye ta 3 ta shigo Najeriya>>Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin taraya ta bayyana a hukumance cewa, Coronavirus zagaye ta 3 ta shigo Najeriya.

 

A Jihar Legas kadai, mutane 30 ne suka mutu dalilin dawowar cutar ta Coronavirus a cikin wata daya da daya gabata.

 

Shugaban kwamitin gwamnatin tarayya dake kula da cutar coronavirus, kuma sakataren Gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya bayyana haka ga manema labarai.

 

Yayi gargadin cewa ana samun yawan masu cutar 500 a kullun tun bayan dawowarta.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *