fbpx
Thursday, August 5
Shadow

Covid-19: ‘Yan asalin kasar Chaina dake zaune a Najeriya kimanin mutum 325 sunyi kaura daga Najeriya

A kalla ‘yan kasar chains 325 ne aka kwashe su daga Najeriya a cikin wani jirgin sama inda jirgin ya nufi Shanghai dake kasar chaina. Hakan na zuwa ne a sakamakon  bullar cutar Coronavirus a kasar.

 

Kasar China ta ebe ‘yan kasarta 325 daga Najeriya ta hanyar jirgin sama na Air Peace wanda aka shirya zai tashi da misalin karfe 10:05 na daren ranar Alhamis.

 

Haka zalika itama kasar Najeriya ta kwashe ‘yan kasarta daga wasu kasashe dake da makwabtaka da kasar.

 

Tun bayan bullar cutar coronavirus kasashe dadama suka fara kwashe al’ummomin su daga kasar wanda suka hada da Kasashe kamar Faransa, Amurka, Ingila, wadanda suka kwashe al’ummomin su tun farkon bullar cutar zuwa kasar Najeriya.

 

Ya zuwa yanzu Najeriya nada akalla mutum 8,000 dake fama da cutar Coronavirus a fadin kasar baki daya.

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *