fbpx
Saturday, October 16
Shadow

Cristiano Ronaldo ya kafa sabon tarihi a Duniyar kwallon kafa

Cristiano Ronaldo ya ci wa tawagar kwallon kafar Portugal kwallo na 112 a wasan sada zumunta da ta doke Qatar 3-0 ranar Asabar.

Dan wasan na Manchester United ne ya fara daga raga a karawar da suka yi a filin wasa na Estadio Algarve.

A watan jiya kyaftin din Portugal mai shekara 36 ya doke tarihin da Ali Daei na Iran ya kafa na cin kwallo 109 a wasannin ƙasa da ƙasa.

Ya zuwa yanzu, Ronaldo ya ɗora tazarar ƙwallo uku kenan a kan wannan tarihin.

Haka kuma wasa na 181 da tsohon dan kwallon Real Madrid ya buga wa Portugal kenan, inda ya doke tarihin Sergio Ramos wanda ke kan gaba a yawan buga wa tawagar ƙasa tamaula a nahiyar Turai.

Dan kwallon Malaysia, Soh Chin, wanda ya yi ritaya a 1984, shi ne kan gaba a tarihin yawan buga wa tawaga wasanni a duniya da wasa 195.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *