fbpx
Thursday, September 23
Shadow

Cutar kwalara ta kashe mutane 100 a jihar Jigawa

Gwamnatin jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar mutane 100 sakamakon barkewar cutar kwalara a kananan hukumomi 19 a cikin jihar.

Babban Sakatare, Ma’aikatar Lafiya ta jiha, Dr Salisu Mu’azu, ya bayyana hakan ga manema labarai a ofishinsa.

Ya ce jihar ta samu cutar kwalara sama da 5,000 a cikin wata daya.

Mu’azu ya bayyana cewa daga cikin adadin, mutane 251 aka kwantar da su a cibiyoyin kiwon lafiya daban -daban a fadin jihar.

Sai dai ya yi gargadin amfani da gurbataccen ruwa, kayan lambu, abincin da ake samarwa daga bakin kogi, yana mai kira da a inganta tsabtar mutum da muhalli.

Mu’azu ya ce gwamnatin jihar, tare da tallafi daga shirin UNICEF da na Lafiya, sun kafa wata tawaga ta gaggawa don dakile yaduwar cutar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *