fbpx
Tuesday, May 18
Shadow

Da Dumi Dumi:Barcelona ta bayyana cewa tana nan daram a gasar European Super League

Shugaban Barcelona, Joan Laporta yayi jawabi akan gasar European Super League inda ya goyi bayan shugaban Madrid Florentino Perez.

 

yawancin kungiyoyi 12 da suka kirkiri wannan gasar sun ja baya akan lamuran tare da bayar da hakuri saboda sukar da gasar ke sha, amma Barca ta bayyana cewa tana nan daram a gasar tare da abokiyar takarar ta Real Madrid.

 

Gabadaya kungiyoyi 12 na gasar Firimiya da suka shiga gasar sun fita kuma suna jiran hukuncin da UEFA zata yanke masu ranar juma’a, yayin da itama Atletico Madrid da Inter Milan suka fita a gasar suka bar Juventus da AC Milan a ciki.

 

Amma maimakin itama Barca taja baya a gasar, shugaban ta Laporta ya goyi bayan shugaban Madrid Perez inda ya bayyana cewa suna nan daram a gasar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *