fbpx
Wednesday, April 21
Shadow

Da dumi-duminsa: An fara yi wa mutum na farko rigakafin cutar Korona a Nigeriya

A yau Juma’a ne Dr. Cyprian Nyong ya zama mutum na farko da aka yi wa allurar rigakafin COVID-19 na Oxford Astra-Zeneca, a Birnin Tarayya Abuja.

 

Dr Cyprian ya kasance ɗaya daga cikin likitocin da ke aikin yaƙar cutar, tun bayan ɓarkewarta a Nigeriya, a watan Maris na shekarar 2020.

 

Ya zuwa yanzu dai shi ne zama jami’in kiwon lafiya na farko da aka yi wa rigakafin tun bayan ƙaddamar da rigakafin a ƙasar nan.

 

wanda za a fi bada fifiko kan jami’an kiwon lafiya da masu taimaka masu wajen yin ta.

 

Babban Sakataren hukumar Lafiya a matakin farko ta Nijeriya Dr Faisal Shuaib ne dai ya yi masa allurar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *