fbpx
Tuesday, May 18
Shadow

Da dumi duminsa: An kashe dan bindingar nan Auwalu Daudawa wanda yayi tubar mazuru

An kashe dan bindingar nan mai suna Auwalu Daudawa wanda ya jagoranci satar daliban makarantar Kankara dake Jihar Katsina.

Auwalu Daudawa shi ne wanda muka kawo maku labarin ya tuba kuma yasa komawa cikin harkar ta’addanci.

Kwamishinan tsaro da lamurran cikin gida na Jihar Zamfara, Abubakar Jastis Dauran ya tabbatar da kashe Auwalu Daudawa ga manema labarai da yammacin Juma’a.

Kwamishinan ya bayyana cewa Auwalu yayi masu ikirarin cewa zai tafi bikin yan uwansa amma abun mamaki ashe cikin daji ya koma, inda daga zuwansa ya gargada gargin shanun wasu Fulani wanda nan take bude masa wuta har lahira.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *