fbpx
Tuesday, August 3
Shadow

Da Duminsa: A karshe dai Sunday Igboho yawa kansa Fada, ya fasa Zanga-Zangar da ya shirya yi a Legas

Me ikirarin fafutukar kafa kasar Oduduwa,  Sunday Igboho ya bayyana cewa,  ya fasa Zanga-Zangar da ya shirya yi a Legas.

 

Hakan na zuwane bayan da aka kama me ikirarin fafutukar kafa kasar Biafra,  Nnamdi Kanu wanda yanzu haka yake tsare a hannun Gwamnati.

 

Sunday Igboho ya yi ikirarin sojoji sun kai samame gidansa a daren ranar Alhamis.  Saidai yace lafiyarsa kalau.

 

A baya dai, Sunday Igboho yace zai yi Zanga-Zangar neman ganin an kafa kasar Oduduwa a garin Legas, abinda ya jawo cece-kuce sosai.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *