fbpx
Thursday, August 5
Shadow

Da Duminsa: An gano manyan hanyoyi 2 da za’a wa Boko Haram illa a gama da ita baki daya

Mutuwar Shugaban Boko Haram,  Abubakar Shekau ta yiwa ‘yan Najeriya da yawa dadi ganin cewa shine jagoran kungiyar data addabi mutane musamman a Arewacin Najeriya da kashe-kashe.

 

Kungiyar ISWAP data balle daga Boko Haram ce ta kaiwa Shekau hari. Wanda hakan yasa ya kashe kansa maimakon ya yadda su kamashi.

 

Shugaban ISWAP, Abu Mus’ab Albarnawi ya bayyana cewa, Shekau ya zabi ya ji kungiyar lahira maimakon ta Duniya.

 

Hakanan ita kanta kungiyar Boko Haram,  Watau yaran Abubakar Shekau sun tabbatar da mutuwarsa inda suka nema masa gafarar Allah.

 

Wanda ya gaji Abubakar Shekau, Bakura Sahaba Modu dan shekaru 24 sannan bashi da kwarewa irin ta Abubakar Shekau.

 

Me sharhi akan ayyukan Boko Haram,  Bulama Bukarti ya bayyana cewa, wannan damace ga Sojojin Najeriya su murkushe Boko Haram gaba dayanta dan a yanzu tana da rauni sosai.

 

Ya kuma bayyana cewa, fada tsakanin Boko Haram da ISWAP bai kare ba, dan kuwa Modu ya jagoranci mayakansa sun kai harin ramuwar gayya akan ISWAP wanda kuma suka kashewa Albarnawi mayaka da yawa.

 

Hakanan kuma, Shima Albarnawi yana fuskantar barazanar tawaye a karkashinsa inda wasu mayakan ISWAP din sam basa jin dadin mulkinsa.

 

Hakanan shima wani me bincike akan ayyukan Kungiyar Boko Haram a cibiyar Bincike dake kasar Faransa, Vincent Foucher na da irin wannan ra’ayi, inda yace fadan dake faruwa tsakanin ISWAP da Boko Haram damace ga sojojin Najeriya su gama da kungiyar, kamar yanda PMnews ta ruwaito.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

1 Comment

  • Sulaiman Shehu Usman

    Shirmen yan median Nigeria kenan, don me ake bayyana ire-iren wannan labari, su yan Boko Haram da Iswap din basa karantawa ne?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *