fbpx
Tuesday, June 15
Shadow

Da Duminsa: An kashe dalibi, an sace malamai 2 da dalibai 3 a Nuhu Bamalli Polytechnic

‘Yan Bindiga sun sace dalibai 3 da malamai 2 sannan suka kashe dalibi daya, yayin da wani ya jikkata yake karbar magani a Asibiti. Lamarin ya farune a jami’ar Kwalejin Ilimin Kimiyya ta Nuhu Bamalli Polytechnic dake Zaria a jihar Kaduna.

 

Lamarin ya farune da misalin karfe 10 zuwa 11 na daren ranar alhamis. Wani dalibi yace ya sun ji harbin bindiga a cikin makarantar amma basu san abinda ya faru ba saboda basa ciki.

 

Sunan wadanda aka sace din sune, Habila Nasai da Malam Adamu Shika. Hakanan an sace mata da ‘ya’ya biyu da wani malam Ahmad Abdullahi, amma an sakosu yau da safe, kamar yanda Rahoton FIJ ya nunar.

 

Wannan dai bashine karin farko da ake samun matsakar tsaro a makarantar ba, inda a halin yanzu ma an nemi dalibai su bar dakunan kwanansu. A shekarar data gabata ma an samu satar matar wani darakta.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *