fbpx
Wednesday, October 20
Shadow

Da Duminsa: Gwamnatin Jihar Kano ta Gano Wani Gidan Yan mari Dake Unguwar yar akwa Naibawa Kano

Tuni dai Kwamishinan Harkokin Addinai tare da Kakakin Rundunar Yan sandan Jihar DSP Kiyawa tare da wasu Jami’an tsaro suka Garzaya gidan suka tarar da Mutane 47 Hudu daga cikin su Dauke da Mari Kada da Hannu An Daure su wasu Kuma Daga cikin Mutanen da aka Daure Duk an Musu rauniki a jikin su tare da farfasa Musu Baya

Inda nan take Kwamishinan Harkokin Addinai na Jihar Kano Malam Baba Inposibble Ya zanta da Wayan da aka Daure tare da azaftar da su sun Bayyana masa Yadda suke wahala ba dare ba Rana Har wani Dalibin Ya bayyana Yadda Dan’uwan sa Ya Rasa Ransa sabi da Wahalar wa a cikin gidan

DSP Kiyawa Mai Magana da Yawun Rundunar Yan sandan Jihar Kano Yace sun ji Labarin gida ne tare da tabbatar masu Abinda suke Ganewa idanuwan su Yanzu Haka tasa suka Kawo harmaki Domin su Ganewa kawunan su Gaskiya Yace Adan Haka Yanzu zasu tafi Da Malam Gidan zuwa Bomai Domin su Kammala Bincike da zarar su Gaba zasu mika su Ga Kotu ta Yanke Hukunci sannan yayi Kira da Dukkanin Masu yin wannan harkar da su dena Domin Kuwa da zarar sun Kama Doka ce zatayi Aiki Akan ka

Kwamishina Yayi Karin Haske Dangane da Masu Gidan Mari Yace Tuni Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ya Rushe Gidajen Mari sannan Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje shima Yace An soke a Jihar Kano Babu wani Gidan Mari Yanzu Idan Har Mutum Yayi laifi tọ a Mikashi Ga Hukuma.

Malam nán da suka kì Fada Mana Gaskiya tun Kafin Faruwar Abun Wallahi Bazsmu Kyale su ba sai Mun Hukunta su sukuma Daliban zamu tafi mu ajiye su zamu Kira Iyayen Kowá mu Danka su A Hannun su

Jaridar Prince24
8/10/2021

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *