fbpx
Tuesday, May 11
Shadow

Da Duminsa: Hukumar DSS Ta Gayyaci Dillalan Shanu Da Abinci Dan jin dalilin da yasa suka daina kai Kayan Abinci Kudu

Jagorancin dillalan Shanu da na Abinci a karkashin hadaddiyar kungiyar masu abinci da noma ta kasa (AUFCDN) a halin yanzu suna tare da jami’an tsaro na DSS.

Babban Sakatare na AUFCDN, Ahmed Alaramma, wanda ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Labour House, Abuja, ranar Litinin, ya ce Shugaban kungiyar, Mohammed Tahir, yana tare da DSS.
Alaramma ya kuma yi zargin cewa jami’an sojan na barazana ga mambobi da kuma kungiyar, yana mai ba gwamnati shawara da ta guji rudani da ke shirin faruwa ta hanyar dakatar da tsoratar da mambobinsu.
Tun farko kungiyar ta sha alwashin ci gaba da yajin aikin na ta a fadin kasar baki daya da kuma ci gaba da tabbatar da aiwatar da shingen kayan abinci da shanu daga shigowa yankin kudancin kasar.
Wannan, a cewarsu, zai dore har sai gwamnatin tarayya ta biya musu bukatunsu, wanda ke kan biyan biliyan N475 na diyyar rayukan mambobi da dukiyoyin da suka yi asara yayin zanga-zangar #EndSARS da rikicin kasuwar Shasa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *