fbpx
Monday, May 10
Shadow

Da Duminsa: Hukumar INEC ta sanar da ranar da za a gudanar da babban zaben 2023

A ranar Laraba ne Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta sanar da ranar da za a gudanar da babban zaben shekarar 2023 mai zuwa.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan a wani taron kwana daya na jin ra’ayin jama’a kan Laifukan Zabe ta Kasa, 2021, wanda kwamitin Majalisar Dattawa kan INEC ya shirya.
Mahmood Yakubu ya ce babban zaben ya rage saura shekara daya, wata tara  makonni biyu da kwana shida ko kuma kwanaki 660 daga ranar da aka bayar da sanarwar, saboda haka ake bukatar yin shiri.
Ya ce an tsara gudanar da zabubbukan a ranar Asabar 18 ga watan Fabrairu, yana mai bayyana cewa cikakken jadawalin zai kasance kafin karshen shekarar.
“A ka’idar da Hukumar ta kafa, Babban zaben na 2023 zai gudana ne a ranar Asabar 18 ga Fabrairu 2023 wanda yake daidai da shekara guda, watanni tara, makonni biyu da kwanaki shida ko kwana 660 daga yau,” in ji shi.
“Muna fatan sakin Jadawalin da Jadawalin Ayyuka don Babban Zaben nan da nan bayan zaben Gwamna na Anambra da aka shirya za a yi a ranar 6 ga Nuwamba 2021.
“Don yin hakan, ya kamata a samu bayyananniya da tabbaci game da tsarin dokokin zabe don gudanar da zaben. Muna da yakinin cewa Majalisar Dokoki za ta yi abin da ya kamata da gaske. ”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *