fbpx
Friday, January 21
Shadow

Da Duminsa: IPOB sunwa ‘yansandan Najeriya yankan rago

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, Kungiyar IPOB tawa ‘yansandan Najeriya yankan rago.

 

Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Muhammad ne ya bayyana haka inda yace kungiyar tsaro dake karkashin IPOB din, ESN ce ta yi wannan aika-aika.

 

A wani bidiyo da ya watsu sosai a shafukan sada zumunta, an ga wasu matasa kusa da gawarwakin ‘yansandan suna musu ba’a har suna cewa daya daga cikin ‘yansandan yayi kama da Fulani.

 

Ya bayyana sunayen wadanda aka sace da Francis Idoko (AP No. 154945); Inspector Emmanuel Akubo (AP No. 222336) and Inspector Rufai Adamu (AP. No. 285009).

 

Ya kuma sha Alwashin cewa, za’a kamo wanda suka yi wannan aika-aika.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *