fbpx
Tuesday, August 3
Shadow

Da Duminsa: Obasanjo zai kafa sabuwar Jam’iyyar siyasa da zata murkushe APC da PDP

Tsohon shugaban kasa, janar Olusegun Obasanjo na shirin fito da wata sabuwar jam’iyyar da zata magance matsalolin APC da PDP.

 

Wata majiya ta gayawa Vanguard cewa, Obasanjo na son hada jam’iyyar ne saboda ya hango da wuya manyan jam’iyyun siyasa na APC da PDP su kai labari.

 

Majiyar tace duk da Obasanjo ya cire hannunsa a harkar siyasa amma yana kokarin ganin ya samo mutum na gari wanda zai zama shugaban kasa a shekarar 2023.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *