fbpx
Tuesday, May 18
Shadow

Da Duminsa: ‘Yan Bindigar da suka sace daliban Kaduna sunce zasu kashe sauran daliban dake hannunsu

‘Yan Bindinga da suka sace daliban jami’ar Greenfield dake jihar Kaduna sun yi barazanar kashe sauran dalibai 17 dake hannunsu.

 

Dalibai 22 ne suka sace da ma’aikaci 1 ranar 20 ga watan Afrilu. A cikin mako 1,’yan Bindingar sun kashe biyar daga cikinsu.

 

A hirar da Shugaban ‘yan Bindigar yayi da VOA Hausa me suna Sani Idris Jalingo yace sun baiwa Gwamnatin jihar Kaduna nan da ranar Talata, ta aika musu Miliyan 100 da sabbin Mashina 10 ko kuma su kashe sauran Daliban.

 

Daga cikin wadanda aka sace din akwai mata 15 da maza 3, cikin mazan akwai jikan tsohon Sarkin Zazzau, Idris, me suna Hamza.

 

Iyayen daliban sun tara Miliyan 55 suka aikawa ‘yan Bindugar amma sun ce sun yi amfani dasu wajan ciyar da daliban kuma wannan shine gargadi na karshe.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *