fbpx
Monday, May 10
Shadow

Da Duminsa:An kama Soja da Tulin makamai a Borno yana shirin Tafiya dasu Abuja

Premium times

Jami’an kungiyar masu tukin Motocin haya ta NURTW sun kama wani Soja da harsasai 2000 cike da wasu Akwatuna.

 

Sojan da aka kama Sunansa Sani Muhammad me mukamin Lance Corporal.  Ya bayyana cewa an bashi izinin barin gurin da yakd aiki, 198 Special Force Battalion saboda rashin Lafiya.

 

Ya bayyana cewa, Abuja zashi, da aka tambayeshi maganar inda ya samo harsasan, yace a wata motar yaki ce data lalace a bataliyar da yake aiki.

 

Saidai Premium times ta ruwaito cewa, da bincike yayi tsanani an gano cewa ba’a baiwa sojan Umarnin barin wajan aikinsa ba. Sannan kuma Hukumar Sojin ta nemi ‘yansanda su mika mata shi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *