fbpx
Friday, May 14
Shadow

Da Duminsa:An kama wanda ke daukar nauyin ‘yan Bindigar dake kai hare-hare a Imo

Rahotanni daga jihar Imo sunce a karshe dai an kama me daukar nauyin ‘yan Bindigar da ke kaiwa ‘yansanda hari a jihar Imo.

 

Mutumin me suna Nnamdi Okafor dan kimanin shekaru 42 na zaunene a Amanaci dake Karamar hukumar Orsu ta jihar.

 

An yi Imanin cewa, Shine ke daukar nauyin ‘yan bindigar da ba’a san ko su wanene ba dake kai hare-hare kan ‘yan Jami’an tsaro. ‘Yan Bindigar dai sune suka kai hari hedikwatar ‘yansandan Jihar Imo da Hedikwatar jami’an gidan yari ta jihar.

 

Vanguard ta ruwaito cewa dama an dade ana nemansa saboda wannan zargi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *