fbpx
Saturday, April 17
Shadow

Da Duminsa:Boko Haram sun kaiwa tawagar Kwamandan Sojojin Najeriya hari inda suka kashe sojoji 2

Rahotanni daga Jihar Borno na cewa kungiyar ISWAP data balle daga Boko Haram ta kaiwa tawagar kwamandan sojojin Lafiya Dole, Majo Janar Farouk Yahya hari.

 

Harin ya farune da a ranar Lahadi a kauyen garin Kuturu dake tsakanin Auno zuwa Jakana, akan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu, Kamar Yanda HumAngle ta ruwaito.

 

A kalla Sojoji 2 majiyar ta samu cewa sun mutu sannan Boko Haram din ta lalata wata motar yakin sojin, saidai babu wata sanarwa kan yawan ‘yan Boko Haram din da aka kashe.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *