fbpx
Sunday, September 19
Shadow

Da Duminsa:Jarumin Fina-finan Hausa ya rasu

Rahotannin da BBC ke samu na tabbatar da rasuwar tauraron fina-finan Hausa na Kannywood Ahmad Tage.

Kafin rasuwarsa ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya, har ta kai ga an kwantar da shi a asibitin Nasarawa da ke jihar Kano.

Tuni ‘yan wasan Hausa na Kannywood suka fara mika ta’aziyyarsu a shafukan sada zumunta.

Ya fi fitowa a fina-finan barkwanci a tsawon lokacin da ya kwashe a harkar, wadda ya fara a matsayin mai daukar bidiyo, kafin daga bisani ya rikide ya zama tauraro.

‘Yan uwansa sun shaida wa BBC Hausa cewa ya rasu ya bar mata biyu da ‘ya’ya 21.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *