fbpx
Tuesday, August 3
Shadow

Da Duminsa:Nnamdi Kanu na bukatar ganin Likita saboda zuciyarsa ta kumbura

Lauyan shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB dake son kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu watau, Efeanyi Ejiofor ya bayyana cewa wanda yake karewar na bukatar ganin Likita.

 

Ya roki gwamnati ta bari likitansa ya ganshi saboda zuciyarsa ta kumbura, Ya kuma bayyana cewa,  Kanu bai ga iyalansa ba tun ranar 18 ga watan July da aka kamashi.

 

Ya kara da cewa sun mikawa hukumar DSS a hukumance cewa Kanun na bukatar ganin Likita saboda zuciyarsa ta kumbura da kaso 13 cikin 100.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *