fbpx
Thursday, August 5
Shadow

Da Duminsa:Sheikh Abduljabbar Kabara ya tuba

Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya nemi afuwar waɗanda suka “fahimci cewa shi ne ya ƙiƙiiri kalaman ɓatanci ga Annabi Muhammadu SAW” da ake zarginsa da yi.

Cikin wani saƙon sauti da ya fitar a ranar Lahadi, an ji malamin na cewa “idan har waɗannan kalamai daga ni suke, ƙirƙirarsu na yi, babu su a litattafai to lallai ya isa babban laifi da ya wajaba a gare ni na gaggauta tuba”.

Ya ƙara da cewa: “Amma idan ba daga ni ba ne, daga cikin waɗancan litattafai ne, to wannan kuma ya zama wani abu daban. Sai mu yi roƙon Allah ya haska wa al’umma su tashi tsaye mu taimaki addininmu, mu fitar da hadisan ƙarya daga ciki domin gudun kar a rusa mana addinin da su.”

Cikin wata hira da BBC, Abduljabbar ya jaddada cewa yana neman afuwar waɗanda suke ganin kalaman da ake cewa ya yi suna ɓatanci ne ga Annabi a wajen fassara hadisan da aka gabatar a wurin muƙabala.

Kalaman nasa na nuni da cewa har yanzu yana nan kan bakansa game da iƙirarin da yake yi cewa ya ciro kalaman ne daga litattafan hadisi.

BBC Hausa ta fahimci cewa shehin malamin ya nemi afuwar ce bayan wasu ɗalibansa sun nemi ya yi hakan.

Cikin hirar da ya yi da BBC jim kaɗan bayan ya nemi afuwar, Abduljabbar ya jaddada cewa yana neman afuwar mutanen da suka fahinci cewa shi ne ya ƙirƙiri kalaman ɓatanci ga Annabi saboda kukan rashin isasshen lokaci da ya dinga yi a lokacin muƙabala.

Ya ce: “Gaskiyar lamari shi ne, sakamakon zaman jiya da aka yi wanda aka takura lokaci da yawa…ba zai yiwu a fitar da irin wannan mummunan al’amari da nake yaƙi da shi ba a minti 10 ko 20, kuma na roƙa [a ƙara] amma ban samu hakan ba.

“Da na ce babu lokaci sai suka tafi a kan cewa e lallai maganar babu ita a hadisai ni ne na yi.

“Idan har wasu sun ɗauka miyagun maganganu irin waɗannan da ake taɓa fiyayyen halitta – waɗanda nake yaƙin fahimtar da al’umma cewa hadisai ne jabu – kuma wasu suke zaton cewa ni na yi, to ya wajaba na nemi afuwarsu bisa wannan zato da suke yi na cewa maganata ce.

“In har tawa ce kamar yadda suka ɗauka, kafin afuwarsu afuwar Allah da mazonsa nake nema.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *