fbpx
Saturday, October 16
Shadow

Da Duminsa:Sojojin kasar Nijar sun ceci na Najeriya yayin da ‘yan Bindiga suka kai musu hari

Sojojin kasar Nijar sun ceci na Najeriya daga hannun ‘yan Bindiga yayin wani hari da ‘yan Bindigar suka kai musu.

 

An ceci Sojojin Najeriya ne a kauyen Basira dake yankin Gidan Roumdji na kasar Nijar din a ranar Juma’a.

 

‘Yan Bindigar sun kaiwa Sojojin harine a sansaninsu dake Burkusuma na karamar hukumar sabon birni ta jihar Sokoto.

 

Sojoji 9 da jami’an NSCDC 3 ne suka mutu a harin kamar yanda Daily Trust ta ruwaito.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *