fbpx
Thursday, July 29
Shadow

Da inje Dubai da sunan hutu, gara in je kasar Nijar>>Rashida Mai sa’a

Tauraruwar fina-finan Hausa,  Rashida Adamu wadda aka fi sani da Rashida Mai sa’a ta bayyana cewa, da ta je Dubai da sunan hutu, gara taje Kasar Nijar ta huta.

 

Tace a Nijar taga Rakuma. Ta bayyana cewa ita Kasuwar Rimi ma ta fi mata Dubai wahalar zuwa, dan sai ta dade bata je Kasuwar Rimi ba amma Dubai tana kwance a Gado zata sayi Tikiti ta samu Visa ta tafi.

 

Tace maganar Bidiyon da tace On Dubai har wasu ke tunanin wai tanawa wanda suka je a wancan lokacin hassada ne ba gaskiya bane, tace wanda suka je din tun suna kananan yara ta je Dubai.

 

Tace ita bata dauki Dubai wajan hutu ba, ta dauki Dubai wajan da zata je ta yi siyayya da kai dinki, tace idan Mutum na son Hutawa to ya tafi faransa, Sifaniya, Amurka ko Jamus.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *