fbpx
Thursday, April 22
Shadow

Daina Kai Abinci kudu: ‘Yan Arewa so suka yi su kashemu da Yunwa, Kuma yaki suke so a yi>>Wani Dattijon Yarbawa

Wani Dattijo daga Yankin Yarbawa, Farfesa Banji Akintoye ya bayyana cewa daina kai Abinci kudu daga Arewa da kuma lalata gonaki da Fulani ke yi a yankin Kudancin Najeriyar, Kokari ne na gangan wajan ganin an saka yankin cikin yunwa.

 

Dan hakane yayi kira ga dattawan yankin da Gwamnoni su tashi tsaye wajan ganin sun kubutar da yankin daga wannan tuggu.

 

Ya bayyana cewa wadannan matakai na Arewa karara yaki take son kaddamarwa akan yankin Yarbawa dan haka dole yankin yayi amfani da duk wata damarsa wajan ganin ya kare kansa.

 

Yace kuma yaki ta hanyar Sakawa Mutum yunwa shine mafi muguntar yaki sannan kuma hakan ya nuna irin kiyayyar da Arewa kewa yankin Nasu. Yace wannan ya kamata ya zama Izina ga mutanen Kudu su tashi tsaye su baiwa harkar Noma Muhimmanci.

 

Yace yanzu da Arewa ta ga cewa yunkurinta na kashe Yarbawa da yunwa bai yi nasara ba, akwai yiyuwar su koma sakawa abincin da suke kaiwa Kudu guba. Yace lalata gonaki da Fulani ke yi a yankin Kudu, Kokari ne na ganin cewa Kudun ta dogara kacokan wajan samun abinci akan Arewa dan su rika yin yanda suke so dasu.

 

Only self-determination will save the Yoruba – Akintoye,’ said, ‘No Yoruba person must now be in doubt that war has been declared against the Yoruba nation, and that we, the Yoruba nation, must be ready to use all our capabilities to defend our nation. This is no longer surreptitious but a glaring and open declaration of war on our people.

 

“War by starvation is the most vicious facet of war. Death by starvation is the most terrible death imaginable. For them to consider starving us at all, the hostility in their spirit against our people must have been terrible. Seeing now that the attempt to starve us to death has failed, we must thoroughly investigate the persistent suspicions of massive food poisoning from the North.”

 

He said, “Obviously, the objective of the Fulani herders and militias for destroying our farms, farmers and farming villages in the past five years has been to force us to become totally dependent on the North for all our food supply so that they may suddenly stop food supplies from the North and thereby plunge us into total starvation and ruin. Now, we have seen how these people will turn anything in which we may depend on them to become weapons against us.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

3 Comments

  • Shafiu Nasiru

    Yanzu wannan farfesan da yake magana yaki Akeso Atayar ta wacce hanya kenan suke nufi? Gaskiya wannnan mutumin yakamata ayi mai gargadi da irin wa ‘yan nan miyagun maganganu na tunzura mata sansu wurin tada Fada na kabilanci. Shin wannnan malamin amatsayinsa na farfesa zaya iya karantar da dalibin da baya ganin girmansa , mutuncinsa , da sauran su. To don haka babu dalilin da zaya sa ‘yan arewa su cigaba da kawo musu abinci suna ci suna Kara jin karfin wulakantasu. To yanzu ga fili ga mai doki sae ku noma kuci ku wulakanta ‘yan uwanku yarbawa. Kuma mu mutanen arewa ba halin mu bane sawa mutane guba a abinciba, halinkune kuma Allah yataimakemu da bamu muke neman wani abu a gurinkuba da kun sakamana guba kamar yada ka fada. Mu ‘yan Arewa bama neman wani tashin hankali ko tada tanzoma, muzan lafiya mukeso a jihohinmu da kuma kasar mu najeriya baki daya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *