fbpx
Wednesday, June 23
Shadow

Dalibai mata 1,833 aka wa ciki cikin kwanaki 90

An dirkawa dalibai mata 1,833 ciki a cikin kwanaki 90 a yankin Tororo na kasar Uganda.

 

Daliban na da shekaru tsakanin 10 zuwa 19, kamar yanda kafar watsa labaran kasar, Daily Monitor UG ta ruwaito.

 

Wani masani a yankin, Mr. Ali Mugerwa ne yayi wannan bincike inda ya bayyanashi a wajan wani taron tattauna matsalolin mata.

 

Lamarin yasa iyaye na shirin dakatar da karatun yara mata a yankin. Masanin ya zargi iyaye da kuma hukuma kan wannan matsala inda yace da iyaye na kula da yaransu yanda ya kamata, hakan ba zata faru ba kuma da hukuma ta samar da yanayin hukunci me kyau shima da wuya hakan ta faru.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *