fbpx
Monday, October 25
Shadow

Daliban da aka sace, ma’aikatan FGC Birnin Yauri, Kebbi sun sake samun ‘yanci bayan kwanaki 118 da aka yi garkuwa da su

An sako dalibai sama da 90 da ma’aikatan Kwalejin Gwamnatin Tarayya (FGC), Birnin Yauri, a Jihar Kebbi.

Wadanda abin ya shafa sun samu ‘yanci bayan sun kwashe kwanaki 118 a tsare.

Idan zaku tuna a ranar Alhamis, 17 ga watan Yuni, kimankn ‘yan bindiga 150 sun mamaye kwalejin tare da yin garkuwa da dalibai sama da 90, da suka hada da maza da mata, da ma’aikata uku, daga ciki akwai mataimakin shugaban makarantar.

Mahaifin daya daga cikin daliban da aka sace, ya tabbatar wa Aminiya cewa an sako daliban, amma bai bada bayanin ko an biya kudin fansa ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *