fbpx
Thursday, December 2
Shadow

Dalilin da ya za a sayar da hukumar layin doga ta Najeriya

Ministar sufuri ta kasar Gbemisola Saraki ta ce za a raba NRC zuwa rassa hudu.

Rahotanni sun ce Ministar Sufuri, Gbemisola Saraki, ta ce Gwamnatin Tarayya za ta raba hukumar kula da layin dogo ta kasar tare da sayarda ita ga ‘yan kasuwa don inganta ayyukanta.

Misis Saraki ta yi magana ne a taron hadin gwiwa na kasa da kasa na Najeriya da aka gudanar a birnin Paris.

Ta ce matakin zai haifar da gogaya a fanin sufuri jirgin kasa, tare da inganta kayayyakin more rayuwa da sauran kadarori.

Ta yi kira ga ‘yan kasuwa na kasashen waje a wurin taron da su lalubo hanyoyin zuba jari a fannin, tana mai cewa matakin zai sake farfado da kimar kamfanin a cikin kasar da kasashen ketare.

“An sabunta alkawuran sufurin jiragen kasa a matsayin wani muhimmin bangare na sauyin zamantakewa da tattalin arziki.

“Abin lura shi ne tsarin tsare-tsare na shekaru 25 da aka yi niyya don gyara duk wani kunkuntar layin dogo da ake da su, da gina sabbin layukan dogo tare da hada sauran tashoshin jiragen kasa .

Sai dai sanarwa na zuwa ne a dai dai lokacin da ma’aikatan jiragen kasa su ka yi barazanar shiga yajin aikin gargadi na kwanaki 3ranar Alhamis mai zuwa.

Ma’aikatan na neman a kara inganta tsarin albashinsu da jin dadinsu da kuma harkokin tsaro da suka shafi hanyoyin jiragen kasan.

BBChausa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *