fbpx
Thursday, December 2
Shadow

Dan Allah karku zabi PDP a 2023>>Gwamna El-Rufai ya roki mutanen Kaduna

Gwamnan jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya, Nasir El-Rufa’i, ya roƙi al’ummar jiharsa kada su zaɓi jam’iyyar PDP a 2023, domin a cewarsa “kada ta ƙara jefa kasar cikin matsalar da ta baro a baya.

Jaridar Vanguard, ta ambato El-Rufa’i na cewa ya kamata jama’a su hadu baki daya domin zaɓar mutumin da zai tsayar da dan takarar gwamnan jihar a zaben 2023, tare da cewa wannan ne lokacin da ya dace ƴan Kaduna su amince da shi da abin da zai zaɓa wa jihar.

Ya kuma yi zargin cewa “idan ba don abin da tsohon Sanata mai wakilar Kaduna ta tsakiya Sanata Shehu Sani da Sulaiman Hunkuyi suka yi ba, wato hana Kaduna ta karbo bashi, da ayyukan ci gaba sun mamaye jihar fiye da wadanda ake gani a halin yanzu.”

A gargaɗin da ya yi wa ƴan Kaduna ya ce “su bude ido da kyau, domin zaɓar abin da ya dace da kuma zai ciyar da su gaba, ba janyo musu koma baya ba.

BBChausa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *