fbpx
Saturday, October 16
Shadow

Dan Najeriya ya lashe Gasar Wakar Larabci ta Duniya

Wani dan Najeriya mai suna Dokta Ahmad Rufa’i ya lashe Gasar Rubuta Waka da Larabci ta Duniya da aka gudanar a kasar Saudiyya.

Shugabar Hukumar ’Yan Najeriya Mazauna Qasashen Waje, Hajiya Abike Dabiri-Erewa ce ta sanar da haka lokacin da take taya shi murnar nasarar da ya samu.
Hajiya Abike ta ce yadda Dokta Ahmad Rufa’i ya doke sauran ’yan takara daga kasashen Larabawa abin a yaba ne. “Muna taya ka murnar wannan nasara da ka samu, musamman ganin ka doke sauran ’yan takara daga kasashen Larabawa. Wannan nasarar abar murna ce ga dimbin ’yan Najeriya baki daya, ba kai kadai da iyalanka. Barakallahu fiha,” inji ta kamar yadda Kakakin Hukumar, Abdur-Rahman Balogun ya sanar.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Wannan gasa da Dokta Ahmad ya lashe, gasa ce da Bankin Musulunci(IsDB) ya shirya domin bikin Ranar Larabci ta Duniya, wadda ta yi daidai da ranar 18 ga watan Disamba, kamar yadda Majalisar Xinkin Duniya ta tanada domin tunatar da duniya muhimmancin Harshen Larabci.

Dan kasar Mauritaniya ne ya zo na biyu, sannan dan Sudan ya zo na uku. Wannan ke nuna cewa daga na daya zuwa na uku duk ’yan Afirka ne.
Aminiya.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *