fbpx
Tuesday, May 11
Shadow

Dan sandan da ya saci bindigogin AK-47 guda biyar ya tsere

An cafke wani dan sanda, Shedrack Aleke Igwe, wanda ke aiki a sashin ajiye makamai na MOPOL base 28, Umuahia, jihar Abia da bindigogin AK-47 guda 5 da ya sata daga dakin ajiyar makaman.

Igwe, wani dan sanda ne, an bayar da rahoton cewa ya yi awon gaba da bindigogi a sashen ajiye makamai tare da taimakon wasu da ba a san ko su waye ba.

An kama shi a karamar hukumar Ikwo ta jihar Ebonyi inda ya fito.

Ya aikata hakan ne a ranar 2 ga wannan watan bayan haka ya tsere zuwa jihar Ebonyi.

Amma bayan kwana biyu, sai rundunar ‘yan sanda daga jihohin Abia da Ebonyi suka cafke tare da tura shi zuwa ofishin’ yan sanda na Jihar Abia don gudanar da bincike.

Tawagar hadin gwiwar daga jihohin biyu ta bi shi zuwa garinsa na Ikwo inda yake buya.

An kama shi nan take tare da taimakon jami’in ‘yan sanda na yankin, Ikwo kuma an fara bincike ba tare da bata lokaci ba.

Biyar daga cikin bindigogin AK-47 da suka bata an kwato su daga hannun shi a Enyibichiri Ikwo da ke jihar Ebonyi.

An kara samun labarin cewa wanda ake zargin kwanan nan ya sayi sabbin babura masu kafa uku don hada-hadar kasuwanci ya ba dan uwansa Ifeanyi Igwe.

An yi amannar cewa watakila ya sayar da wasu riffles din, in ba duka bindigogin AK-47 da ya yi nasarar saya ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *