fbpx
Friday, April 23
Shadow

Dangote Ya Kaddamar Da Cibiyar Horar Da Direbobi, Don Rage Hadduran Hanya

Kamfanin simintin Dangote ya kaddamar da Cibiyar Horar da Direbobi ’a Kamfanin Siminti na Dangote (DCP), Obajana, Jihar Kogi don magance hatsarin sufuri a hanya.
Ta kuma horar da direbobi 50 a cibiyar. A yayin taron taron a karshen makon da ya gabata, Shugaban Cibiyar Horar da Direbobi, Mista Harisson Pepple, ya ce horarwar ta yi daidai da tsarin kamfanin na kawo karshen haɗarin mota.
Mista Pepple ya ce an fitar da direbobin da suka samu horon ne daga yaron mota da suke da su, kuma lokacin ba da horon wata shida ne.
Ya nuna kwarin gwiwa cewa “ranakun hatsarin da ya shafi manyan motocin Dangote a kidaye suke”.
“Shirin Direbobi Masu Koyon Aikin ya kunshi komai. Makonni goma sha biyu na farko na koyarwa ne a aji. Sannan akwai zuwa koyan aiki na wata uku, ”inji shi.
Ya ce, an kirkiro wannan tunani ne na sabuwar Cibiyar Koyar da Direbobi, a watan Yunin shekarar 2020, da nufin horarwa, da sake horas da su, da kuma jan hankalin direbobin na Dangote.
Ya kuma sanar da cewa kamfanin yana yin wasu rukunin kwararrun direbobi da lasisin Class G, yana mai jaddada cewa kamfanin na yin duk mai yiwuwa don kawar da kansa daga hadarurruka.
A cewarsa, kamfanin yana hada gwiwa da Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) a cikin mafi yawan ayyukanta, ya kara da cewa an kuma koyar da direbobin da ke horar da dabarun tuki na kariya, wanda ya hada da tuki don ceton rayuka, lokaci da dukiya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *