fbpx
Wednesday, January 26
Shadow

Dangote Ya Sake Zama Wanda Ya Fi Kowa Kudi A Afrika A Karo Na Tara A Jere

Hamshakin mai kudin Nijeriya kuma Bakano, shugaban kamfanin Dangote Group, Alhaji Aliko Dangote ne mutum mafi arziki a Nahiyar Afrika a shekarar 2020, kamar yadda rahoton Forbes ya nuna.

Wannan shine karo na tara a jere da attajirin ya zarcewa dukkan masu halin Nahiyar.
Jerin masu kudin ya mayar da hankali kan kasashen Afrika takwas masu kudi; yayinda kasar Masar da Afrika ta kudu suke da masu kudi biyar-biyar a jerin, Najeriya na da hudu, sannan kasar Maroko mai biyu.
Rahoton ya bayyana cewa Alhaji Aliko Dangote ya zo na daya da arzikin dala bilyan goma ($10.1 billion) na kasuwancinsa a Siminti, man fetur, flawa, Timatur da Sukari, 
Sai Nassef Sawiris na kasar Masar mai arziki dala bilyan takwas ($8 billion) ya zo na biyu, 
Sai Mike Adenuga mai kamfanin sadarwan Glo ya zo na uku.
‘Yan Nijeriyan da suka shiga jerin masu kudin nahiyar sabanin Dangote sune Abdul Samad Isyaka Rabiu, Mike Adenuga, da Folorunsho Alakija.
Ga jerin masu kudin nan:
Aliko Dangote $10.1 billion
Nassef Sawiris $8 billion
Mike Adenuga $7.7 billion
Nicky Oppenheimer $7.7 billion
Johann Rupert $6.5 billion
Issad Rebrab $4.4 billion
Mohamed Mansour $3.3 billion
Abdulsamad Rabiu $3.1 billion
Naguib Sawiris $3 billion
Patrice Motsepe $2.6 billion
Koos Bekker – $2.5 billion
Yasseen Mansour – $2.3 billion
Isabel dos Santos – $2.2 billion
Youssef Mansour – $1.9 billion
Aziz Akhannouch – $1.7 billion
Mohammed Dewji – $1.6 billion
Othman Benjelloun – $1.4 billion
Michiel Le Roux – $1.3 billion
Strive Masiyiwa – $1.1 billion
Folorunsho Alakija – $1 billion


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *