fbpx
Friday, May 14
Shadow

Dara taci gida:Nnamdi ya aika a kashe me gidansa, Shugaban MASSOB>>Yace ‘yan IPOB ne ke kaiwa Ofisoshin ‘yansanda hari

Shugaban kungiyar dake son kafa kasar Biafra,  MASSOB, Ralph Uwazuruike ya bayyana cewa shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB,  Namdi Kanu ya aika masa ‘yan Bindiga su kasheshi.

 

A wani bidiyo da ya wallafa wanda ya yadu sosai kamar wutar daji, Ralph bayyana cewa, Kanu yana tunanin jami’an tsaronsa irin na gwamnatin Najeriya ne?

 

Yace idan akwai wanda ya kamata ya sanshi sosai, to Nnamdi Kanune, yace Kanu Matsoracine sosai, domin shine ya reneshi, yace shine ya bashi kudin auren da yayi, yace ya bashi kudi Dubu 450 yayi aure, amma kuma shine zaiwa haka.

Wasu manya dai ciki hadda gwamnonin Inyamurai sun rika fadar cewa ba kungiyar IPOB ce ke kai wadannan hare-haren ba amma yanzu dai gashi sun tonawa kansu Asiri.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *